
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Asabar ne Hukumar gudanar da jarrabawar makarantun sakandare ta yammacin Afirka, wato WAEC, ta sanar da fitar da sakamakon jarrabawar rukunin farko na ɗaliban babbar sakandare da suka yi a komfuta ta shekarar 2025.
Hukumar ta wallafa hakan ne a shafinta na X, inda ta ce na ɗaliban makarantu masu zaman kansu ne aka fitar.
Ana gudanar da jarrabawar ne da ake kira da Computer-base a makarantun gwamnati da masu zaman kansu domin zamanantar da tsarin jarrabawa ga ɗaliban wanda ake yi a kowace shekara.
