Taron Buɗe-Baki: Sheikh Imam Gana ya gana da ‘yan jarida a Jos

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

Babban malamin addinin Musuluncin nan na garin Jos, wanda kuma shi ne daraktan ilimi na ƙungiyar JIBWIS a Jihar Filato, Sheikh Imam Abubakar Bala Gana, ya gayyaci taron manema labarai na ciki da wajen Nijeriya, domin shan ruwa na buɗe baki a gidansa, a wani ɓangare na ƙoƙarin jawo ‘yan jarida jiki don cigaba da yaɗa saƙonnin zaman lafiya da haɗin kan al’ummar Jihar Filato da malamin ya saba isarwa.

Malamin ya buƙaci manema labarai su riƙa kusantar malamai don sauraron saƙonnin da suke isarwa ga al’umma a cikin karatunsu da wa’azozinsu, domin su sanar wa duniya gaskiyar abin da malaman ke faɗa ba jita-jita ba. Ya ce, duk malamin da ya san abin da yake yi, ba zai yi wasa da ‘yan jarida ba. Domin malamai abokan ‘yan jarida ne.

Ya ce, sai ‘yan jarida ƙwararru ne suka san muhimmancin tace bayanai da faɗar gaskiya, ba labaran ƙarya da jujjuya magana ba. Don haka ya gayyaci ƙungiyar ‘yan jarida ta NUJ da abokan aikinsu domin ƙulla zumunci da ƙarfafa aiki tare.

Ya kuma yabawa Gwamna Caleb Mutfwang bisa ƙoƙarin da yake yi wajen tabbatar da cigaban zaman lafiya da ƙarfafa zaman tare a tsakanin ƙabilun Filato baki ɗaya. Yayin da ya roƙi Kirista da Musulmi da ke azumin Ramadan da na Lent su sanya Gwamna da Jihar Filato cikin addu’o’in su, musamman yanzu da musulmi suka shiga goman ƙarshe na azumin Ramadan.

Shugabar Ƙungiyar ‘yan jarida ta NUJ a Jihar Filato, Ayuku Pwaspo, ta yaba sosai da gudunmawar da Sheikh Imam Gana yake bayarwa ga cigaban zaman lafiya a jihar da kuma tallafin da yake bai wa NUJ a koda yaushe.

Tsohon Kwamishinan Watsa Labarai Dan Manjang ya ƙalubalanci gwamnati mai ci da ta kira irin wannan ganawa da ‘yan jarida da sauran al’ummar jiha, domin yin buɗe baki da ƙarfafa zaman lafiya.

By ukarofi