
Daga BELLO A. BABAJI
An kama wani jami’in soja da wani ɗan sanda mai suna Ajiye Joel bisa laifin sace wasu batira daga Hukumar Jiragen ƙasa ta Ƙasa (NRC) tare da wani jami’in hukumar a Jihar Kaduna.
Sahara Reporters ta ruwaito cewa, wani jawabin ƴan sanda ya nuna cewa dakarun sojojin atisayen ‘Fansan Yamma’ ne suka kama mutane ukun a ranar 19 ga watan Maris.
Dakarun haɗaka na atisayen, an ware su ne musamman don daƙile ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.
Tuni dai aka tsare su a reshe na ɗaya na jami’an sojoji dake Kaduna yayin da ake gudanar da bincike akan su.
Hakan na zuwa ne watanni kaɗan da korar wasu sojoji biyu masu suna CPL Innocent Joseph da L/CPL Jacob Gani bisa sace wayoyin lantarki, wato armoured cables a turance a Matatar Ɗangote, a Legas.
