Ƙungiyar SERAP ta maka Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a kotu kan dakatar da Gwamnan Jihar Ribas, mataimakinsa da mambobin Majalisar Dokokin jihar, wanda ta kira haramtacce da kuma saɓa wa kundin tsarin mulki. SERAP ta ce dakatarwar ta biyo bayan ayyana dokar ta-ɓaci a jihar, wanda shugaban ƙasa ya yi ba tare da cikakken bin ƙa’ida ba.
Waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Yirabari Israel Nulog, Nengim Ikpoemugh Royal da Gracious Eyoh–Sifumbukho, waɗanda ke cikin ƙungiyar lauyoyin masu rajin kare hakkin jama’a na SERAP (SVLN) a Jihar Ribas. A cewar ƙarar da aka shigar a babbar kotun tarayya da ke Abuja, masu ƙarar na neman a soke dakatarwar, tare da ƙalubalantar naɗa Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (Rtd) a matsayin mai kula da harkokin jihar.
Lauyan da ya shigar da ƙarar a madadin masu ƙarar, Ebun-Olu Adegboruwa (SAN), ya bayyana cewa dakatar da shugabannin da aka zaɓa cikin dimokuraɗiyya a Jihar Ribas ya saɓawa dokar ƙasa, musamman ma tanadin sashe na 305 na Kundin tsarin mulki na 1999 da aka gyara. Ya kuma jaddada cewa dimokuraɗiyya ba za ta yi tasiri ba idan aka ci zarafin ‘yancin jama’a na shiga cikin harkokin mulki da kuma bin doka da oda.
