
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar ADP ta bayyana damuwarta akan babban zargin da ke yawo acikin al’ummar Nijeriya cewa an shigo da sinadarin ‘thallium sulphate’, wanda guba ne mai haɗarin gaske.
A cewarta, matuƙar hakan ya tabbata, zai iya zama barazana ga tsaron ƙasa da zaman lafiyar al’ummar Nijeriya.
A wata sanarwa daga Shugabanta na Ƙasa a ranar Litinin, ADP ta ce wannan ba al’amari ba ne da za a siyasantar da shi domin abu ne ya shafi zaman lafiya don haka wajibi ne hukumomi su yi abin da ya dace wajen ganin an daƙile dukkan barazanar da hakan ka iya haifarwa a Nijeriya.
Ta bayyana cewa, a yanzu ba za ta yanke hukunci ba akan labaran da ake yaɗawa akan al’amarin daga gidajen jaridu ko shuru daga hukumomin da ke da alhakin ɗaukar mataki a kai. Haka kuma a tafiyar tsarin dimukraɗiyya da ke gudanar da lamuransa bisa tsarin dokar ƙasa.
ADP ta bayyana cewa, ‘yan Nijeriya na buƙatar amsoshi na gaggawa kuma gamsassu daga Ofishin mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (ONSA), akan ko an taɓa amince wa shigo da sinadarin, an siyo, an shigo da shi, an adana, ko kuma a bisa wane dalili idan har zargin ya tabbata.
Haka kuma, ta kirayi hukumomi masu alhalin bincike akan al’amarin da su tabbatar da gabatar wa al’umma cikakken bayani a kai su da kwamitocin majalisar dokokin wajen tseratar da al’umma hatsarin sinadarin.
Kazalika, ta yi gargaɗi ga hukumomin Nijeriya akan haɗarin yin shuru, wanda hakan zai sanya alamar tambaya game da kiyaye tabbatar da gaskiya da adalci.
