
Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Nijeriya ta umarci Musulman ƙasar su fara azumin Watan Ramadan a ranar Laraba 18 ga watan Fabrairun 2026.
Matakin na alamta shigar watan Ramadana mai alfarma – wanda musulmi a faɗin duniya ke gudanar da ibadar azumi, ɗaya daga cikin shika-shikan musulunci biyar.
Cikin wata sanarwa da fadar Sarkin Musulumin ta fitar a ranar Talata da daddare ya ce an samu bayanan ganin watan a wurare daban-daban a ƙasa.
Don haka ne fadar ta sanar da Laraba 18 ga watan Fabrairu a matsayin ranar 1 ga watan Ramadana na 1447AH.
