Wani sabon harin bom ya kashe mutane 10 a Borno

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Aƙalla mutane 10 sun mutu yayin da wasu 10 suka jikkata sakamakon fashewar wani bom da aka ɓoye a hanyar Maiduguri–Damboa, a ƙauyen Komala, Jihar Borno. Harin ya auku ne da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin Laraba, inda wata motar ɗaukar kaya kirar Suzuki ta taka na’urar fashewa da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne suka dasa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin ƙwararru na jihar da ke Maiduguri don samun kulawar likitoci.

Ya bayyana cewa waɗanda suka mutu su huɗu ne, yayin da sauran goma ke fama da rauni iri daban daban.

Wasu shaidu sun bayyana cewa harin ya haifar da cunkoso mai tsanani a hanyar, inda fasinjoji da direbobi suka maƙale na tsawon lokaci. Wani fasinja ya bayyana cewa sun ɗauki lokaci mai tsawo kafin su wuce wajen da abin ya faru saboda cunkoso da ruɗani.

Wannan hari na baya bayan nan ya zo ƙasa da watanni biyu bayan irin wannan fashewar IED a yankin da ya halaka mutane takwas tare da jikkata wasu 11.

Hukumar tsaro ta ce tana gudanar da bincike kan yawaitar dasa bama-bamai a hanyar Maiduguri–Damboa, wacce ta kasance ɗaya daga cikin hanyoyin da suka fi fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda a jihar.

By ukarofi