
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City Jeremy Doku ya ce har yanzu City tana da amannar cewa za ta iya farfaɗowa dafa lallasar da Real Madrid ta yi mata a karawar farko da suak yi a tsakaninsu a gasar Zakaran Nahiyar Turai, wato Champions League.
A cewarsa, akwai buƙatar magoya bayan City su sanya matsi ga ‘yan wasan Madrid, yana mai cewa a ƙwallon ƙafa komai na iya faruwa don haka suke ganin za su iya yin nasara a wasa na biyu da za a fafata a filin Etihad.
Hakan na zuwa ne kwanaki biyu da Madrid ta hannu Ɗan wasa Federico Valverde ta casa City da ci 3 da nema a filin Santiago Bernebau.
A ranar Talata za a haɗu a karawa ta biyu a wasan da City ke neman ƙwallaye uku rigis kafin wasan ya koma ɗanye, yayin da ɓangarorin ke neman gurbi a rukunin wasannin dab da na ƙarshe.
