Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Hukumar Presidential Compressed Natural Gas Initiatiɓe (PCNGi), Ismaeel Ahmad, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na ƙara ƙaimi wajen faɗaɗa amfani da gas (CNG) da kuma motocin lantarki (Eɓ) domin rage tsadar sufuri da al’ummar Nijeriya ke fuskanta.
Ismaeel Ahmad ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda suka tattauna kan yadda hauhawar farashin man fetur a duniya, musamman sakamakon rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, ke shafar farashin sufuri a Nijeriya.
A cewarsa, ya gabatar wa shugaban ƙasar cikakken bayani kan shirye-shiryen da hukumar ke yi na faɗaɗa cibiyoyin cika gas (refuelling stations) a sassa daban-daban na ƙasar domin sauƙaƙa wa masu ababen hawa amfani da gas maimakon man fetur.
Ya ƙara da cewa shirin ya haɗa da samar da kayan canza motoci daga fetur zuwa gas (CNG conɓersion kits) domin bai wa masu ababen hawa damar sauyawa zuwa amfani da gas wanda ya fi araha.
Ismaeel Ahmad ya kuma bayyana cewa shirin na PCNGi ya haɗa da samar da sabbin babura masu ɗaukar fasinjoji uku (keke napep) da ke amfani da gas, domin tallafa wa hanyoyin sufuri masu rahusa ga jama’a.
Bugu da ƙari, ya ce hukumar na kuma shirin kafa cibiyoyin cajin motocin lantarki (Eɓ charging stations) a sassa daban-daban na ƙasar domin ƙarfafa amfani da motocin lantarki a Nijeriya.
A cewarsa, babban burin wannan shiri shi ne rage kuɗin sufuri ga ’yan Nijeriya, tare da ƙara bunƙasa amfani da gas da lantarki a matsayin hanyoyin makamashi masu araha a harkar zirga-zirga.
Ya jaddada cewa idan aka aiwatar da shirin yadda ya kamata, zai taimaka wajen rage dogaro da man fetur, da kuma sauƙaƙa wa al’umma wahalar da suke fuskanta wajen biyan kuɗin sufuri.
