Daga UMAR GARBA a Katsina
Wata ƙungiya a Jihar Katsina ta ce, wasu kwamandojin ‘yan bindiga da dama sun miƙa wuya sakamkon shiga tsakanin da ta yi a sulhun da aka yi da su.
Kungiyar ta ce, ‘yan bindigar da kansu ne suka nemi a yi sulhu tare da amincewa za su dakatar da kai hare-hare kodayake wasunsu ba su ajiye makamansu suna riƙe da su a matsayin kariya.
Shugaban ƙungiyar Kwamared Hamisu Sai’idu Batsari shi ne ya tabbatar wa da BBC waɗannan bayanai a tattaunawa da shi.
Ya ce daga cikin jiga-jigan ko kacallolin da suka miƙa wuya akwai, irin su Abu Radda da Maikada da Umar Blak da Tukur ɗannajeriya tare da yaransu.
”Kowannensu musamman shi Abu Radda za ka iya samun shi da yaran da suka kai 500 a ƙarƙashinsu,” ya ce.
Ya ƙara da cewa, ”su kuwa su Tukur Mairaƙumi da su Maikada su Tukur ɗannajeriya su kuma za ka iya samunsu da yaran da suka kai ɗari bibbiyu ko ɗari uku kowannensu.
Kwamared Hamisu ya ce, a zaman sasancin da suka yi da waɗannan ɓarayin daji, wasu daga cikinsu suna riƙe da makamai ne kawai da sunan suna son samun tabbacin za a ba su kariya su da dabbobinsu daga wasu daga cikin barayin da su ba su yarda da sulhunba, idan suka mika wuya.
Shugaban ya ce suna da ƙwarin gwiwa na samun zaman lafiya daga wannan sulhu domin a cewarsa, ‘yanbindigan ne a wannan karon da kansu suka nemi sulhun saɓanin na baya da ake nemansu a yi musu wasu alƙawura da kuma ba a cikawa, wanda hakan ke sawa su koma ruwa a can baya.
Daga cikin sharuɗɗan da ya ce sun cimma da ɓarayin dajin akwai cewa, dakatar da ayyukan ta’addanci da suke yi sannan su saki dukkain waɗanda suka kama ba kuma lalle sai na wannan yanki ba.
Sa’idu Batsari ya kuma ce su a ɓangarensu ‘yan bindigan sun nemi gwamnati ta tabbatar da adalci a tsakaninsu tsakanin su mazauna daji da sauran al’umma ta fuskar sama musu abubuwan more rayuwa, kamar ruwan sha da makarantu da sauransu.
”Sannan sai kuma sai bangaren jami’an tsaro ‘yanbindigan sun nemi da a daina kamasu haka kawai ana kashe su, ba tare da wani laifi ba, in kuma sun yi laifi a kama su a gurfanar da su gaban shari’a a yi musu hukunci kamar yadda doka ta tanadar,” inji shi.
