Masana kimiyya a Jamus sun ƙera wata sabuwar fasaha da ke amfani da siginar WiFi wajen gane mutum ba tare da amfani da kyamara ko na’urar ɗaukar hoto ba.
A cewar masu binciken, fasahar na nazarin yadda siginar WiFi ke canjawa yayin da mutum ke motsawa ko tafiya a wani wuri. Ta hanyar amfani da ƙirƙirarriyar basira ta AI, tsarin na iya bambance mutum daga wani da kusan cikakkiyar daidaito.
Masanan sun bayyana cewa wannan cigaba na iya taimakawa wajen inganta tsarin tsaro, kula da tsofaffi da marasa lafiya a gidaje, da kuma ayyukan ceto a lokutan gaggawa.
Sai dai kuma, binciken ya tayar da muhawara a tsakanin masu kare haƙƙin sirri, waɗanda ke nuna damuwa kan yiwuwar amfani da fasahar wajen sa ido kan mutane ba tare da saninsu ko amincewarsu ba.
