
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Taron addu’ar bankwana da Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas ya shirya ya samu ɗaukewar ƙafa na wasu muhimman mutane a jihar musamman ga rashin ganin Ministan Abuja Nyesom Wike da dakataccen gwamna Siminalayi Fubara.
A jiya Lahadi aka gudanar da taron a wani coci da ke Fatakwal, babban birnin jihar yayin da kantoman ya ke shirin barin ofis duba da wa’adin dakatarwar wata shida da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Fubara a watan Maris ya zo ƙarshe.
A yayin jawabinsa na bankwana, Ibas ya yi gargaɗin koma wa rikicin siyasa da jihar ta tsinci kanta aciki kafin zuwansa, yana mai kira ga ƴan siyasa da su guji abinda ka iya mayar da jihar gidan jiya.
A ranar 18 ga watan Maris, 2025 Shugaba Tinubu ya naɗa VA Ibas (mai ritaya) a matsayin kantoman Ribas sakamakon dakatarwar da ya yi wa zaɓaɓɓun jami’an gwamnatin jihar bayan ƙamarin rikicin siyasa a tsakanin su.
Duk da cewa taron addu’ar ya samu halartar manyan sakatarori, ciyamomi, jagororin hukumomin tsaro da na wasu hukumomi, Wike, Fubara, sarakunan gargajiya da wasu jiga-jigan ƴan siyasa ba su samu zuwa ba, lamarin da ya haifar da cecekuce.
Ibas ya kuma miƙa godiyarsa ga Shugaba Tinubu, hukumomin tsaro da al’ummar jihar bisa goyon da haɗin kai da suka ba shi a yayin jagorancin da aka ɗora masa.
