Wike ya zargi Amaechi da nuna fuska biyu kan sabuwar Dokar Zaɓe

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya zargi tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, da sauran jagororin ’yan adawa da nuna fuska biyu kan sabuwar Dokar Zaɓe ta 2026 da aka rattaba wa hannu.

Yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, Wike ya mayar da martani kan sukar da ’yan adawa ke yi wa wasu tanade-tanaden dokar, musamman sashen da ya ba da damar watsa sakamakon zaɓe ta hanyar hannu idan na’urar lantarki ta ƙasa aiki sakamakon matsalar sadarwa.

Wike ya yi iƙirarin cewa a lokacin gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wasu daga cikin waɗanda a yau ke goyon bayan watsa sakamako ta hanyar lantarki, sun yi adawa da shi, suna masu cewa zai iya jawo musu shan kaye a zaɓe.

“Ku tuna a zamanin Buhari lokacin da batun watsa sakamako ta lantarki ya taso. Mutane irin su Rotimi Amaechi suna cikin gwamnati. Sun ce kada a sanya hannu, domin idan aka yi hakan za a rasa zaɓe,” inji Wike.

Ya tambayi dalilin da ya sa a yau waɗannan mutane suke nuna tsananin goyon baya ga watsa sakamako ta lantarki, yana mai cewa matsayinsu na yanzu ya dace ne da buƙatun siyasa ba da ƙa’ida ba.

Ministan ya jaddada cewa Dokar Zaɓe ta 2026 ba ta soke watsa sakamako ta lantarki ba, sai dai ta samar da wata kariya domin kada a tauye haƙƙin masu kaɗa ƙuri’a a yankunan da ke fama da matsalar sadarwa.

“Ba su ce a daina watsa sakamako ta lantarki ba. Abin da aka ce shi ne idan aka samu matsala — kuma hakan na iya faruwa — kada a hana a ƙirga ƙuri’un jama’a,” inji shi.

Game da tanadin da ya wajabta zaɓukan fidda gwani kai tsaye a cikin jam’iyyu, Wike ya ce hakan zai rage tasirin masu kuɗi da manyan ’yan siyasa a harkokin cikin gida na jam’iyyu. A cewarsa, zaɓukan fidda gwani na kai tsaye na ba wa mambobin ƙasa damar taka rawa, sabanin na wakilai da kan bai wa gwamnoni da masu ruwa da tsaki damar mamaye tsarin.

Ya kuma soki ’yan Nijeriya da ya kira “kwararrun masu ƙorafi”, yana mai cewa a baya sun koka kan zaɓukan wakilai saboda yadda suke ƙarfafa manyan jiga-jigan siyasa, amma a yanzu suna sukar gyaran da aka yi domin faɗaɗa dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyu.

A makon da ya gabata, jam’iyyun adawa ciki har da ADC da NNPP sun buƙaci Majalisar Tarayya ta sake duba dokar, suna masu cewa wasu sassa na cikinta “masu tauye dimokuraɗiyya ne” kuma na iya rage gaskiya da amincewar jama’a ga tsarin zaɓe.

Baya ga muhawarar Dokar Zaɓe, Wike ya kare matakin da ya ɗauka na sanya dokar hana fita kafin zaɓen ƙananan hukumomin Abuja na ranar 21 ga Fabrairu. Ya ce a matsayinsa na Ministan Abuja — wanda ya kwatanta da “gwamnan” yankin — yana da ikon ɗaukar irin wannan mataki domin tsaro, kuma an amince da hakan daga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Sai dai Sanata Ireti Kingibe, mai wakiltar Abuja ta bayyana dokar hana fitar a matsayin mataki na kama-karya, tana mai cewa duk wani takunkumi mai faɗi kan zirga-zirga ya kamata ya kasance bisa hujjoji masu ƙarfi da cikakkiyar fahimta daga ɓangarori daban-daban.

Wike ya kuma zora laifin rashin shirin zaɓen ƙananan hukumomi kan ’yan adawa, yana mai cewa nasarorin da APC ta samu alama ce ta goyon bayan jama’a ga gwamnatin Tinubu.

Al’amuran sun ƙara ruruta muhawara kan Dokar Zaɓe ta 2026, musamman game da daidaita buƙatar gaskiya da sahihancin zaɓe da kuma kare ’yancin dimokuraɗiyya a Nijeriya.

By ukarofi