Daga IBRAHIM MUHAMMAD a KANO
Kungiyar Tsofaffin ɗalibai na Makarantar Horas da Malamai ta Mata ta Kano (WOTCOSA) da yanzu ake kiran ‘makarantar da Goverment Girls College’ (WTC), ’yan aji na 1975 sun gudanar da taron cika shekaru 50 da kammala makaratar.
Taron tsofaffin ɗaliban da aka gudanar a harabar makarantar ranar talata ya haɗa da buɗe ɗakin karatun makarantar da aka gyara aka sanya littafai da fitulu da fankokin masu aiki da hasken rana da kujjeru da kuma gyara masallacin makarantar da mai ɗakin tsohon Gwamnan jihar Kano tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ɗaya daga cikin tsofaffin ɗaliban ta ɗaukin nauyi aka yi.
A yayin taron ƙungiyar tsofaffin ɗalibai ta WOTCOSA ta karrama Uwargidan tsohon Gwamnan jihar Kano Farfesa Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje da tagwayen lambobin yabo bisa irin ɗinbin gudummawa da take baiwa cigaban ƙungiyar da makarantar tasu da harkar ilimi da kuma irin karancin ta da jinƙan al’umma.
A jawabinta a taron Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana cewa taron nasu abin jin daɗi da farin ciki ne, suna godewa Allah bisa yarjewa da yayi har yanzu suna tare da juna da zumunci tsakaninsu wanda hakan rahama ne daga Ubangiji da yayi a gare su, domin mafi yawa wasu ɗaliban idan an gama makaranta an watse kenan sai dai ka haɗu da ko maƙocinka ko ɗan’uwa da kuke kusa.
Ta ce yanzu irin zumunci da suke dashi a tsakaninsu suna halartar bikin aure da suna a tsakaninsu, yaransu ma da suka taso idan lokacin aure ya yi suna haɗuwa ana biki ta kai ma yanzu har na jikoki ake zuwa suna godiya ga Allah da ya bar su da rai da lafiya ya basu iko suka yi tattaki na kusa dana nesa suka zo makarantar da suka gama shekaru 50.
Farfesa Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta ce duk wani abu da yake faruwa Allah ne yake ƙaddarawa ya yi amfani da bawa ne wajen taimakawa al’umma irin abinda suke tarbiyya ce da suka tashi da ita daga iyaye da kakanni kuma Allah ya taimaka ya bata mai gida Kamilalle, bawan Allah. Dakta Abdullahi Umar Gandije da suka zauna tare suka ƙirƙiro Gidauniyar Gandunje da a ƙarƙashin ta suke kyautatawa al’umma kama daga gina masallaci da makarantu,musuluntar da maguzawa da kula da harkar lafiya a fannoni daban-daban wannan ƙarfin gwiwa ne da Allah ya bada shi da kulawar iyaye.
Ta yi nuni da cewa a baya can iyayensu sun hango inganci na karatu lokacin da aka zaɓosu su aka kawo su makaranta duk da ana nuna damuwa akan tura yara karatun boko a lokacin don fargaban kada su rasa tarbiyya amma iyayensu suka gane neman ilimi da mace da namiji duk abune mai muhimmanci, kuma ya kasance da yanda aka ɗora tarbiyyar yaro a gidansu
Ta yi kira ga iyaye akan su tashi tsaye su sanya ido akan tarbiyyar ya’yansu maza da mata tun suna ƙanana saboda a abokantaka a da su iyayensu sun san gidan da yaro zai tafi an san wajenda zai je, idan wani yazo an san ɗan wane gida ne yazo, amma yanzu kula da hakan abin yayi sauƙi, dole ayi waiwaye abin nan na baya da aka bari na kyautata tarbiyya a dawo dashi don inganta tarbiyyar yara domin yaran nan sune arziki da zamu yi alfahari dasu yakasance sun hau hanya yanda yakamata su riƙe ilimi na addini da na zamani, sai wasu abubuwa marasa daɗi da yake faruwa Allah ya kawar da su kuma kowa na da gudummawa da zai bayar Allah kuma zai kawo ɗauki .
A nata jawabin Shugaban tsare tsare na kwamitin gudanar da taron cika shekaru 50 na WOTCOSA.
Hajiya A’isha Ja’afar Yusuf ta ce wannan buki gagarumine duk da ba shine na farko da tsofaffin ɗalibai na makarantar horon malamai na aji na 75 sukayi ba.Su da sukayi makarantar mafi yawa sunyi malanta na aji da yawansu sun yi shugaban makarantun sakandare dana furamare har Allah ya kai mafi yawansu zuwa manyan matsayi duk a tafarkin koyarwa.
Ta ce duk wanda akace yau yana cika shekaru 50 da gama makarantar abin godiya ne ga Allah don makarantar ta yaye ɗalibai da suka zama manyan mutane da yawa sun godewa malamansu da suka riƙe su a lokacin ajujuwa biyu ne ma, yawanci kowane aji mutum 20 zuwa sama ne a ciki baya kaiwa 30 akwai lokaci na kulawa da yara sosai malamansu turawane ma mafi yawa.
Ta ce daga ɗalibai yan ajin su akwai matar Dakta Abdullahi Umar Ganduje tsohon Gwamnan Kano.Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje da wata matar wani Gwamnan ma da farfesoshi da manyan likitoci, lauyoyi, ’yan siyasa da ɗalibai da dama da suke kan manyan matsayi a fagage da dama
Hajiya A’isha Ja’afar Yusuf ta ƙara da cewa akwai wani taro da suka taɓa yi a baya suka kira shi “ka dawo da kujerarka” saboda a shawo kan ƙarancin abin zama a makarantar da Farfesa Hafsat ta ji ita ta yiwa duka ajin kujeru guda 60 sai ta zo ta baiwa makarantar gadaje da katifu har da kuɗi tana yin abubuwa da yawa a makarantar.
Ta ƙara da cewa, sai kuma gashi ta yunƙuro bayan makarantar tayi ɗan ƙorafi na ɗakin karatu ga ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na WOTCOSA ta kai kujeru da kantar zuba littatafai da litattafai har lantarki mai aiki da hasken rana tasa da fankoki haka ma tayi a masallaci kuma kasancewar shi ilmi kogi ne duk abinda ka zuba masa zai haɗiye ,ba kawai kuɗi ba duk taimakonda aka kawo ga yara zasu ɗauka kuma zai zama sadaka mai gudana.
Hajiya A’i’sha Ja’afar Yusuf tayi nuni da cewa shi tarbiyya daga gida ake farawa don haka tayi kira ga iyaye su jajirce akan tarbiyyar ‘ya’yansu idan sun je makaranta malamai ne suke ɗawainiya da su idan sun koma gida iyaye su sa ido domin zamani ya canza, kuma Allah ya halicci mata su kula da tarbiyya da tsaftar yara a gida su basu ilimi, domin shi ilimi in babu tarbiyya shirme ne, in aka gino tarbiyya daga gida sai ɗaliba ta zo sauran yara ma ƙaru.
