Daga HABU DAN SARKI a Jos
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu ya yi kira ga hukumomi a Nijeriya da su tabbatar da ganin an samar da wani tsari da zai riƙa tantance malamai da fastoci masu wa’azi, har da masu kafa ƙungiyoyin addini, domin magance matsalar yaɗa koyarwar da ba ta dace da addini, kundin tsarin mulkin ƙasa, da zaman lafiya ba.
Babban basaraken na magana ne a wajen taron tunawa da cika shekaru 50 da ziyarar da babban malamin addinin Musuluncin nan Shaihu Ibrahim Inyass ya kai Jos, babban birnin Jihar Filato, bisa gayyatar tsohon shugaban Nijeriya Janar Yakubu Gowon, domin jaddada saƙon musulunci game da zaman lafiya da tarayya tsakanin sauran addinai.
Sarki Sanusi wanda ya gabatar da wata lacca mai taken, ‘Yadda za a cimma zaman lafiya a tsakanin al’umma masu bambancin addini ko ƙabila’, ya bayyana cewa, wasu daga cikin matsalolin da ƙasar nan ke ciki na da nasaba da barin al’amuran addini a sake babu linzami, ta yadda kowa ya ga yana da dama ko ya yi karatu sai ya hau mimbari ya fara wa’azi da yaɗa baƙin aƙidu da ke da matuƙar haɗari ga zaman lafiyar al’umma.
Ya ce, babu inda addinin Musulunci ya ba da damar ɗaukar doka a hannu ko tayar da fitina ga kowa, amma wasu na jirkita koyarwar addini don haddasa fitina, saboda son zuciya da cimma wata mummunar manufa da sunan addini.
Addinin Musulunci yana da daɗaɗɗen tarihin kyakkyawar zamantakewa da ya yi da mabiya addinin Kirista, tun farkon Hijira zuwa ƙasar Habasha, kuma wannan alaƙa ta cigaba da gudana tsawon lokaci, har bayan sahabbai, in ji Sarkin Kano.
Ya nemi al’ummar Filato maza da mata su zauna lafiya da juna cikin girmamawa da fahimtar juna, ba tare da sake komawa lokacin rikice-rikice da zubar da jini ba.
Ya tabbatar wa Gwamnan Jihar Filato Caleb Mutfwang cewa, Musulmi a jihar za su ba da dukkan goyon bayan da ake buƙata, don samun ɗorewar zaman lafiya, matuƙar za a cigaba da kiyaye haƙƙokin su da ba su dukkan wata dama da kundin tsarin mulkin ƙasa ya basu.
Wannan saƙo na zaman lafiya da adalci shi ne Mai Martaba ya riƙa isarwa a tarukan da ya halarta cikin kwanaki uku da ya yi a Jos. Ya samu damar halartar ganawa da Gwamnan Jihar Filato, majalisar sarakunan gargajiya ta jiha, da kuma gidan marayu. Sannan ya gabatar da huɗuba da jan sallar Jumma’a a Babban Masallacin Jumma’a na Jos, ya kuma jagoranci Zikirin Jumma’a da ganawa da ƙungiyoyin ýan ɗariƙa daban-daban.
Sarkin Kano, wanda harwayau shi ne Khalifan Tijjaniyya na Nijeriya, yana tare ne da wasu daga cikin mambobin majalisar sarki ta Kano, da wasu manyan shaihunan ɗariƙa daga jihohin Nijeriya daban-daban.
