Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
ɗan Saran Kano, Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass, ya bayyana muhimmancin barin shari’a a ƙasar nan ta riƙa cin gashin kanta domin zai daƙile irin katsalandan da wasu masu faɗa a ji ke yi mata.
Ya ce abin takaici ne a harkar shari’a a ƙasar nan a ce wani daga gefe ko gwamnati na juya abubuwa hakan na faruwa ne sakamakon maƙure tafi da shari’ar da hanasu cin gashin kansu kullum sai dai faɗa a baki don haka su na fata a samu yin komai bisa ƙa’ida.
Gambo ɗanpass wanda ya ce matsalar rashin tsaro a ƙasar nan na da alaƙa da yadda talauci da yunwa da rashin aikin yi da ake fama dashi idan za a kyautata tsarin tattalin arziƙi a farfaɗo da kamfanoni da suka durƙushe a samu aikin yi kasuwanni su bunƙasa to za a samu sauƙin barazanar tsaro.
Ya yi kira ga jama’a su cigaba da yin addu’o’i da jajircewa akan neman mafita kowa ya san halin da ake a ciki na yunwa da fatara da rashin aikin yi sai anyi gyara an bai wa kowa haƙƙinsa an baiwa jami’an tsaro da masu Shari’a damar su an talallawa harkar kasuwanci da harkar noma kowa ya samu ya tsaya da ƙararsa sai a ga sauyi mai amfani.
Alhaji Gambo Muhammad ya yi nuni da cewa yanzu saboda tsananin tsadar aikin hajji ta kai mutane sun kasa biya amma akwai ƙasashe irinsu Ghana da su ka ɗauki mataki na rage kuɗin Makka tunda aka rantsar da shugaban ƙasar wanda tun a wajen yaƙin zaɓensa ya ce in yayi nasara zai rage kuɗin Makka yanzu ya kafa kwamiti don ganin an samu rangwame.
ɗanpass ya ce amma anan ƙasar tamu da shugaba da mataimakin sa duk Musulmi ne amma maimakon shugaban ƙasa ya tashi tsaye ya nemo rangwame amma sai gashi ma ƙari aka yi akan kuɗin, gashi mutane na son zuwa amma ya gagara saboda tsada yakamata Gwamnati ta duba yadda za ta rage a samu sassauci da mutane za su je.
