Yadda ƴan zanga-zanga su ka mamaye gidan Buhari a Katsina

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Yayin da zanga-zangar tsadar rayuwa ke cigaba da cabewa a faɗin Nijeriya, a na zaman ɗar-ɗar sakamakon tururuwa da masu zanga-zangar su ka yi a gidan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da ke Daura da jihar Katsina.

Hakan na zuwa ne bayan da zanga-zangar ta sauya salo zuwa tashin tashin-tashina a sassa daban-daban na faɗin ƙasar wanda hakan ya sanya jihohi uku su ka sanya dokar hana fita.

An ga wata ɗaukar bidiyo dake nuna ƴan zanga-zangar maƙil a gidan Buhari inda wasu ke ƙoƙarin kutsawa cikin gidan yayin da wasu kuma ke ihun “Bama yi! Bama yi! Bama yi!” saboda matsin rayuwa da ake fama da shi a ƙasar.

Ganin haka ya sa wasu su ka fito domin kwantar da hankulan fusatattun matasan inda ya buƙaci su wakilta mutum ɗaya ya yi magana a madadin su domin gabatar wa Buhari.

Baya ga haka ne sai su ka garzaya zuwa ga Fadar Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar Farouk inda a nan ne aka harbi ɗayan su a ƙafa, amma hakan bai sa sun ja da baya ba.

Haka nan, sun ƙona ofishin jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Dutsinma tare da lalata tutar jam’iyyar a ofishinta da ke ƙaramar hukumar Katsina.

A wani artabu da aka yi tsakaninsu da ƴan sanda, an kashe ɗaya daga cikin ƴan zanga-zangar da kuma raunata wani ɗan sanda.

Bugu da ƙari, sun yi ta jifar jami’an tsaro a kewayen gidan gwamnatin jihar a lokacin da wasu ɓata-gari su ka shiga cikin tafiyar.

A lokacin da ya ke magana game al’amarin, mai magana da yawun rundunar ‘Yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq ya gasgata batun ƙona ofishin jam’iyyar a Dutsinma, sai dai ya ce ba su samu rahoton kisa ba.

By Babaji