Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mutane aƙalla 19 ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin bom ɗin Ƙungiyar Boko Haram a teburin wani mai shayi a Jihar Borno.
A daren Laraba ne mayaƙan ƙungiyar suka tayar da bom ɗin a teburin mai shayin da jama’a ke hira a garin Kawuri da ke Ƙaramar Hukumar Konduga.
Wani jami’in gwamnatin jihar ya ce mutane da dama sun samu raunuka a sakamakon tashin bom ɗin da misalin ƙarfe 8.05 na dare.
Jami’in gwamnatin ya ce, hatta waɗanda abin ya rutsa da su ba za su iya faɗin haƙiƙanin yadda abin ya auku ba.
Ya bayyana cewa, “Babu wanda zai ya cewa ga abin da ya faru, amma mun fi kyautata zaton dasa bom ɗin aka yi, ba harin ƙunar baƙin wake ba.
“Mun gano gawarwakin mutane 19, amma ba mu tantance yawan waɗanda suka samu raunuka ba.
“An kai waɗanda suka ji raunin asibiti a Maiduguri domin ba su kulawa.”
Ƙoƙarin wakilinmu ba samun tsokaci daga ɓangaren hukuma kan lamarin bai yi nasara ba.
Wakilinmu a Maiduguri ya kira kakakin ’yan sandan Jihar Borno, DSP Kenneth Daso, domim samun ƙarin haske amma wayarsa ba ta shiga.
Harin ya auku ne kwanaki uku bayan ƙungiyar ta kai hari a wani ofishin ’yan sanda inda ta kashe wani ɗan sanda da wata mata, suka kona motoci biyu a garin Jakana da ke ƙaramar hukumar.
Kimanin awa 24 bayan ya nakiyar da kungiyar ta dasa ta tashe wani jami’in kuɗi a ma’aikatar ilmin jihar bayan motarsa ta taka bom ɗin a kan babban titin.
Yankin Kawuri na da nisan kilomita 50 daga garin Maiduguri a kan babbar hanyar Maiduguri -Konduga- Bama.
Nakiyar da motar jami’in ta taka ta kuma jikkata mutane da dama.
