Yadda aka gudanar da taron ranar ‘Yaumul Ƙur’an’ da Marigayi Khalifa Isyaku Rabiu ya assasa

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An gudanar da taron ‘Yaumul Ƙur’an’ na bana a masallacin Juma’a na gidan Khalifa Isyaka Rabiu wanda ya samu halartar alarammoni da dama daga ciki da wajen jihar Kano.

Taron da ake gudanar da shi duk shekara Marigayi Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu ne ya assasa shekaru da yawa kamar yadda ɗaya daga cikin masu shirya taron Alhaji Auwalu Isyaka Rabiu ya shaida wa manema labarai..

Ya ce ba zai iya sanin takamaimai lokacin da aka soma gudanar da taron na ‘Yaumul Ƙur’an’ ba tun suna yara ake tara bayin Allah su karanta Alƙur’ani domin yi wa ƙasa addu’ar samun zaman lafiya da yalwar arziƙi da kariya daga dukkan abin ƙi akan haka yake bayan kuma komawarsa ga Allah su kuma ‘ya’yansa suka ɗora akan abin da ya yi musu wasiyya akansa.

Ya ce shi ya sa aka taru bana ma aka yi saukar karatun Ƙur’ani 3,300 kuma suna sa ran baɗi ma za a ƙara fiye da haka da yardar Allah.

Ya ƙara da cewa karatun da ake taruwa a yi na Yaumul Ƙur’an tun kafin akai ga wannan sigar ya san an kai a ƙalla sama da shekaru 30 ana yi, amma dai da irin wannan sigar a zauna tun lokacin da aka buɗe masallacin Juma’a na Ƙofar Mata da a can ake har Allah ya sa aka dawo masallacin gidan Khalifa sama da shekara 30 ake duk shekara ba a taɓa fashi ba.

Malam Auwalu Isyaka Rabiu ya ce dama irin karatu da ake a gidan Khalifa da na darasu a tarihi da suka samu ya kai shekaru da yawa ana yi domin shi ma Khalifa gada ya yi daga wajen mahaifinsa Malam Rabiu Allah ya jaddada musu rahama su kuma ‘ya’ya Allah ya sa su cigaba da ɗorawa akai.

Malam Auwalu ya ce wannan karatu ana yi ne saboda Allah da kyakkyawan ikilasi ba wata buƙata sai ta neman Allah ya bamu zaman lafiya akan haka Khalifa ya assasa kuma akan haka suka ci gaba da yi an yi shine domin Allah ya bai wa ƙasar nan lafiya da yalwar arzƙi.

Malam Auwalu Isyaku Rabiu ya ce Ƙur’ani shine ginshiƙi na addinin Musulunci shine annabtar da Allah ya turo Manzon Allah da ita shine zancen Allah da in kaji shi ba wani kauce-kauce zance ne na Ubangiji saboda haka dukkan burin Musulmi ya zamana ya yi tamassuki da Ƙur’ani kuma abinda zai gayawa ‘yan uwa kowa ya rike Ƙur’ani wanda ya same shi ba wani matsayi da Allah ba zai kai shi ba.

Shi ma Malam Musbahu Rabiu ɗaya daga cikin yan kwamitin taron ya ce taron an saba yinsa duk shekara tun Khalifa yana raye aka kuma ci gaba da gudanarwa da shi bayan rasuwarsa cikin waɗanda suka halarci taron akwai babban limamin masallacin Sheikh Ahmadu Tijjani dake Ƙofar Mata Sheikh Nasir Adam da Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran malamai daga ciki da wajen Kano.

By ukarofi