Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Hukumar makarantar yaran sojoji maza da ke garin Jega a Jihar Kebbi ta karrama maigirma gwamnan jihar Kebbi Malam Nasir Idris.
An gudanar da bikin karramawar ne ranar asabar a lokacin da makarantar take gudanar da bikin yaye ɗalibai makarantar.
Hukumar makarantar ta bayyana cewa ta bai wa Maigirma Gwamna wannan karramawar ne bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban makarantar da kuma ilmi bakiɗaya.
Shugaban Ma’aikatan Jihar Kebbi Alhaji Safiyanu Garba Bena ne ya wakilci Maigirma Gwamna Dakta Nasir Idris a wurin taron bikin yaye ɗaliban. Ya bayyana jin daɗinsa bisa ga yadda hukumar makarantar ke aiwatar da tsare-tsaren ta da kuma tuntuɓar gwamnatin jihar a duk lokacin da buƙatar haka ta taso.
Bena, a madadin maigirma gwamna Nasir ya miƙa kyautar kuɗi naira milliyan talatin ga hukumar makarantar tare da bayar da tabbacin gwamnatin jihar a shirye ta ke da bai wa wannan makarantar goyon baya.
Ya ƙara da cewa wannan karramawar ba Maigirma Gwamna kaɗai aka karrama ba an karrama al’ummar jihar ne bakiɗaya.
