Farfesa Sa’adatu Liman tana kawo ci gaba a babbar Jami’ar Nasarawa, cewar Farfesa Maikano

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Lafiya 

An yaba wa sabuwar shugabar babbar Jami’ar Jihar Jihar Nasarawa dake garin Keffi a jihar Nasarawa, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman dangane da ci gaba da ta kawo jami’ar a yanzu cikin lokuta ƙalilan da ta yi a muƙamin sabuwar shugabar babban jami’ar ta gwamnatin jihar.

A lokacin wani zantawa na musamman ne da wakilinmu ya yi da Farfesa Maikano Ari wanda a yanzu haka shine shugaban fannin karatu na gaba wato Post Graduate Studies a Turance na babbae jami’ar ne ya bayyana haka a ofishinsa dake jami’ar ranar Laraba 31 ga watan Yulin shekarar 2024 da ake ciki.

Farfesa Maikano Ari bayyana cewa ba shakka tunda shugabar jami’ar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta fara aiki a matsayin ta fara ne da ƙirƙiro tare da aiwatar da wasu kyawawa da muhimman ƙudurori dake cigaba da kawo cigaba masu ma’ana kawo yanzu a jami’ar.

Ya ce ba shakka Farfesa Sa’adatu kawo yanzu tana cimma burin ne ta tattauna akai-akai da sauran shugabanni da ma’akatan jami’ar inda a ƙarshe bayan ta fahimci ƙalubalen da kowane fannin ke fuskanta sai nantake ta fara ƙirƙiro tare da aiwatar da wasu kyawawan mafita tare da goyon bayan sauran shugabannin a duka matakai.

Har ila yau Farfesa Maikano Ari ya ci gaba da bayyana cewa bayan waɗannan nasarori da aka samu a jami’ar ta gwamnatin jihar kawo yanzu cikin lokaci ƙalilan da ta yi, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman takan kuma jagoranci sauran shugabanni da ma’aikatan jami’ar akai-akai inda sukan tafiya lungu-lungu da saƙo-saƙon jihar ta Nasarawa dama wajen jihar don neman haɗin kai da sauran hukumomi da suka dace musamman a fannin ilimi don tabbatar da bunƙasar harkokin ilimi a jami’ar baki ɗaya inda ya kuma yi amfani da damar ya yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da zaƙulo tare da naɗin Farfesa Sa’adatu Liman ɗin a matsayin sabuwar shugabar jami’ar cewar gwamnan bai yi zaɓin duhun dare ba. Idan za a iya tunawa dai a ‘yan kwanakin baya ne gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ya nada mace tafarko wato ita Farfesa Sa’adatu Hassan Liman a matsayin sabuwar shugabar babban jami’ar ta gwamnatin jihar.

By ukarofi