Yadda aka kashe mutum 64 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Aƙalla mutum 64 ne aka kashe a cikin kwanaki biyu a jihar Sokoto yayin da ’yan bindiga suka kai farmaki.

Adadin waɗanda suka mutu a hare-haren na ranar Lahadi da Litinin a ƙaramar hukumar Goronyo da ke jihar ya ƙaru zuwa 43 daga 15, yayin da wasu 14 suka mutu a ranar Talata a hare-haren da aka kai a ƙauyukan ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar.

Harin na baya-bayan nan wanda aka kashe mutane 14 ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin tura ƙarin kayan aikin soji zuwa jihar domin magance matsalar rashin tsaro.
Wani mazaunin unguwar Sabon Birni da ya tabbatar da faruwar harin, ya ce, ‘yan bindiga sun mamaye wasu ƙauyuka a gundumar Unguwan Lalle a daren ranar Talata.

A cewarsa, sun kashe wani mutum Abdullahi Usman a Unguwan Lalle, mutum tara a ƙauyen Tsangerawa, huɗu kuma a Tamindawa.

Ya ƙara da cewa, “sun kuma buɗe wuta kan wata mota a ƙauyen Gajid, inda suka kashe mutane uku ciki har da direban.”

Majiyar ta ce, fasinjoji biyar ne suka samu raunuka a harbin bindiga, a halin yanzu kuma suna samun kulawa a wani asibiti.

An kuma ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane uku a wannan ƙauyen.

Daga baya an sako mutanen bayan yarjejeniyar da aka yi cewa, mutanen yankin za su biya harajin Naira miliyan biyu nan da ’yan kwanaki.

Sai dai kwamishinan ‘yan sandan jiha, Kamaluddeen Okunlola ya ce, maharan sun kashe mutane takwas.

A hirarsa da manema labarai, Kwamishinan ya ce, “sun kai hari a wasu ƙauyuka masu nisa da ba a iya isa saboda rashin hanya. Amma da yardar Allah za mu same su. Muna bibiyarsu.”

An tattaro cewa a wani samame da aka kai da daren Lahadi zuwa wayewar garin ranar Litinin, an kashe mutane 13 a garin Illela da ke kan iyaka da jamhuriyar Nijar sannan an kashe mutum biyu a Goronyo mai tazarar kilomita 76 gabas da Sokoto.

Sai dai adadin ya ƙaru zuwa 43 a Laraba lokacin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi bayani a ziyarar ta’aziyyar da ya kai Illela.

A baya dai Gwamna Tambuwal ya bayyana maharan a matsayin ‘yan bindigan kuma a matsayin ‘yan ta’adda, yayin da shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da harin, ya kuma ce, sojoji su yi amfani da na’urori na zamani domin zaƙulo maharan.

A cikin wata sanarwa a ranar Laraba mai ɗauke da sa hannun mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Muhammad Bello, Tambuwal a ziyarar da ya kai garin Illela ya bayyana hare-haren a matsayin abin tayar da hankali.

Ya ce, “wannan ba ƙaramin abu ba ne, Wannan lamarin ya tava mu sosai.”

Sai dai ya yaba wa ƙananan hukumomi da sarakuna da shugabannin al’umma bisa yadda suka shirya jami’ansa kai da ke aiki tare da jami’an tsaro a yankin bisa doka.

Ya roƙe su da kada su karaya da harin na baya-bayan nan. ya ce, ya kamata hakan ya zaburar da su domin su ruɓanya ƙoƙarinsu.

Gwamnan ya ba su tabbacin taimakon gwamnati a duk lokacin da ake buƙata, yayin da yake addu’ar Allah ya jiqan waɗanda suka mutu.

Idan za a iya tunawa, gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin dakatar da harkokin sadarwa a sassan jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina da Kaduna, domin mayar da martani ga ’yan bindiga da suka addabi yankin Arewa maso Yamma.

Sai dai wasu masana na yin kira da a sauya salo domin masu aikata laifuka suna tafka laifukan da suka haɗa da garkuwa da mutane da kuma yi wa mata da ƙananan yara fyaɗe a daidai lokacin da mutanen yankin ke fama da wahalar damar kiran waya don neman tallafi.