Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tun a shekarar 2024 ma’aikatun sadarwa ke kira da a ƙara kuɗi, inda suka ce ɓangaren na cikin haɗarin durƙushewa idan ba a ƙara kuɗi ba kamar yadda ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya sha bayyana cewa gwamnatin tarayya ita kaɗai “ba za ta iya ɗaukar nauyin tallafin wutar lantarki ba,” ya ƙara da cewa “ba zai yiwu ba.”
’Yan Nijeriya da suka zanta da wannan jaridar Blueprint sun nuna matuƙar damuwarsu kan ƙarin kuɗin wutar lantarki da na sadarwa, ba tare da sanar da tsayayyen lantarki ba.
Sun ce ƙarin kuɗin yana ci musu tuwo a kwarya a kasuwancinsu da kuma kuɗaɗen da suke kashewa duk wata.
Wani make kafe a Abuja, Sunday Iwuanyanwu, ya ce kuɗin wutar da yake biya a duk wata ya haura daga N15,000 zuwa N25,000, duk da rashin samar da tsayayyen wutar lantarki. Iwuanyanwu ya koka da yadda wutar lantarki a yankinsa ya ragu sosai zuwa ƙasa da sa’o’i biyar a kullum.
Ya ce, saboda rashin wutar lantarki, ‘yan kasuwa sun fi dogaro da jenareta da ke amfani da man fetur don gudanar da ayyuka, lamarin da ya sa ya riƙa kashe aƙalla Naira 20,000 a kullum kan man fetur don sarrafa janaretansa, baya ga kuɗin kula da injin.
Wani malami mai ritaya, Hassan Maiika, ya bayyana cewa “mafi yawa kuɗin wutan lantarki ba kasafai yake daidai da yadda ake amfani da wutar lantarkin ba, abin da ƙasar nan ke buƙata shi ne doka mai ƙarfi da Majalisar Dokoki ta ƙasa ta yi don kare ‘yan Nijeriya daga cin zarafi daga masu samar da wutar lantarki”.
Ita ma wata mai makaranta mai zaman kanta, Miriam Haskenu ta ce, makarantar ta ta fi dogaro da injin janareto wajen tafiyar da harkokinta.
Ta ce makarantar ta yi shirin sanya na’urorin sola masu amfani da hasken rana domin taimakawa wajen rage tsadar lantarki.
Wani kwararre a fannin samar da lantarkin sola da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an samu ƙaruwar masu son lantarkin sola, biyo bayan ƙarin kuɗin wutar lantarki.
Owen Egbunu, wanda ya mallaki gidan biredi, ya koka da tsadar man dizal, inda ya ce ya dogara da janareta mai amfani da dizal ne zai iya cimma burinsa na samar da burudi, la’akari da yadda ake samun wutar lantarki a yankinsa.
Egbunu ya ce, ƙarin kuɗin wutar lantarki, ta fuskar samar da wutar lantarki, yana kawo babbar illa ga harkokin kasuwanci a ƙasar, don haka ya kamata a magance shi.
