Jaridar Blueprint Manhaja ta yi nazari tare da tattaro bayanai dangane da tarihin rikicin Maitatsine.
Rikicin Maitatsine ya faro ne a ranar 11 ga watan Disambar shekarar 1980, a unguwar Malafa. Malafa unguwa ce daga gabas, ta yi iyaka da unguwar Fagge wacce ta ke da mashahuran mutane masu arziki, malamai da ’yan kasuwa da sauransu, misali a ɓangaren masu arziki akwai irinsu Alhaji Garba A.D. Inuwa, da Alhaji Sama’ila maiguza.
An haifi Marwa Maitatsine a cikin shekarar 1924. Kodayake a iya bincikenmu ba mu gano ainihin iyayen Maitatsine ba, amma bincike ya tabbatar da cewa, Marwa Maitatsine mutumin ƙasar Kamaru ne, amma Maitatsinen yana ikirarin cewa shi mutumin ƙauyen Jabbi ne wacce take cikin tsohuwar jihar Gongola, a yanzu jihar Adamawa.
Yana ɓoyewa da jihar Gongola ne saboda yadda yake sarrafa harshen Fulatanci, amma da aka zurfafa bincike an gane Maitatsinen ƙarya ya yi Maitatsine ɗan wani ƙauye ne mai suna Jappa a arewacin ƙasar kamaru, garin yana kan iyaka tsakaninsu da Nijeriya.
Shi Maitatsine ɗan ƙabilar Mufu ne waɗanda mafi yawansu ba Musulmai ba ne, ba su da addini, Maguzance suke bi. Maitatsine ya shiga addinin Musulunci a cikin shekarar 1940 A lokacin yana ɗan kimanin shekaru 16 a duniya. A wancan lokacin ya bar ƙauyansu ya nufi Marwa.
Garin marwa, gari ne na ‘yan ƙabilar Mufu, kafin Fulani su zo su mamaye shi, shi ya sa Fulatanci ya zama shi ne harshen mutanan garin.
Har Maitatsine ya kai fiye da shekaru 16 yana muguwar al’adar nan ta tsafi, da bautar gumaka, amma Maitatsine bai bar bautar gunki ba, da duwatsu. Suna ɗinka kambuna da manyan layu, Ga su da irin kau-da-bara, da sagau, ga su da cin baƙin tauri, wuƙa ba ta kama su.
Su kan yanka ma dodo, ɗan adam ma’ana su ma su kan zubar da jini irin waɗannan tsafe-tsafe da camfe-camfe. Maitatsine ya taso da shi, ya kuma riƙa yi har da ya zo Kano, Maitatsine ya fara zama yaron gidan wani Balarabe ne mai suna Mohammad Arab, wanda shi ne ya Musuluntar da Maitatsinen.
Bayan bayyanar Maitatsine, da yawan mutane sun ɗauka sa’a ta yi kusa, tunda Dujal ya bayyana, rana kawai suke jira ta fito ta yamma, ta faɗi a gabas.
Maitatsine baƙi ne tsamurarre mara jiki, tsawonsa zai kai mita 1.7. Sannan ba shi da tsage a fuskarsa, yana da haƙorin gwal guda biyu a bakinsa, wanda ya sa shi ne a Makka a shekarar 1970. Maitatsine, ya isa Kano ne, cikin shekarar 1955, nan da nan kuma ya fara wa’azi.
Bayan farko-farkon samun yancin Nijeriya, lokacin ne sha’anin na Maitatsine ya fara ta’azzara. Lokacin hankalin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Sir Muhammadu Sunusi ya juyo kan Mai tatsinen. Sunusi ya sa aka fidda Maitatsine daga Kano, bai ma tsaya nan ba, Sarkin sai da ya tabbatar da cewa an mai da shi ƙasarsu ta Kamaru a cikin shekarar 1962. Bayan da Maitatsine ya koma can ƙasarsu ta Kamaru ya ci gaba da yaɗa wannan ɓarna, yana baɗala.
Bayan Marwa na wancan lokacin Lamido Yaya Hammadi ya kore shi cikin shekarar 1963, ya sake dawowa garin Kano, bayan murabus ɗin Sir. Sunusi, Maitatsune ya komo Kano da aƙidar Qur’ani Zalla. Maitatsine yana da’awar shi Annabi ne, kuma yana ganin kansa kamar mujaddidi Shehu Usman ɗanfodio.
Maitasine yana da aƙidar Qur’ani Zalla, yana inkari ga hadisi da sunnar Manzon Allah (SAW) kuma yana hani ga karanta wani littafi in ba Qur’ani ba, Maitatsine yana ganin aiki da kayan bature haramun ne kamar su rediyo, agogo, kekuna, motoci da sauran su.
A shekarar 1979, ya fara wannan da’awar ta shi, inda yake kiran kansa annabin Hausa a ‘yan tsakanin shekarun 1978 zuwa 1979, inda ‘yan sandan Nijeriya suka sake kama shi. Sannan aka kama yaransa wato ’yan tatsine.
Rundunar sojojin Nijeriya ta ba da sanarwar kimanin mutane dubu biyar 5,000 ne suka rasa rayukansu a rikicin Maitatsine cikin har da shi kanshi Maitatsinen da jama’arsa.
Maitatsine ya mutu sakamakon wani rauni da aka yi masa, wasu kuma sun ce ciwon zuciya ne ya kashe shi.
