Tare da CHIROMA AMINU ASID
Illar cin abinci a cikin leda ko kuma ‘takeaway’ na soso na da illa da dama ga lafiya, musamman idan an zuba abinci mai zafi ko mai maiƙo a cikinta.
Illolin da yake haifarwa:
1. Ciwon daji (cancer):
Lokacin da leda ta haɗu da zafi sosai, tana fitar da wasu sinadarai masu guba (kamar BPA da phthalates) da ke iya shiga abinci. Waɗannan na iya ƙara haɗarin cutar daji idan ana yawan amfani da su.
2. Cututtukan ciki:
Abincin da ya haɗu da sinadarai daga leda na iya haddasa tashin zuciya, gudawa, ko matsaloli a hanji.
3. Illa ga hanta da ƙoda:
Wasu sinadarai daga leda na iya taruwa a cikin jiki, suna jawo illa ga hanta da ƙoda.
4. Illa ga masu juna-biyu (pregnancy):
Ga mata masu juna-biyu, yawancin abinci daga leda na iya shafar cigaba ko girman jariri tare da kawo naƙasu (tawaya ko ‘deformity’) ga jaririn da za su haifa.
Saboda haka, yana da kyau a guji zuba abinci mai zafi ko mai maiƙo a cikin leda.
A riƙa amfani da kwanon ƙarfe, roba maras guba (‘BPA-free’) ko tangaran ko wasu nau’o’in kayan zuba cin abinci, waɗanda aka amince da su.
Riga-kafi ya fi magani.
Chiroma Aminu Asid,
(SAN, EHO, CPM, AESM, ACHRM PGD-HRM)
