Yadda Arewacin Nijeriya ya fi fama da matsalar ’yan mata masu ɗaukar ciki – Rahoto

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani sabon rahoto kan lafiyar al’umma ya bayyana cewa matsalar ɗaukar ciki a tsakanin ’yan mata ƙanana na ci gaba da zama babban ƙalubale ga lafiyar jama’a a Nijeriya, musamman a jihohin arewacin ƙasar kamar Kebbi, Zamfara da Kaduna, inda aka ce ake samun mafi yawan adadin wannan matsala.

Rahoton, mai taken Rahoton Halin Lafiyar ƙasa na 2025, wanda aka fitar a ranar Lahadi a Abuja, an samar da shi ne ƙarƙashin dokar Dokar Kiwon Lafiya ta ƙasa ta shekarar 2014. Rahoton ya yi nazari kan yanayin lafiyar haihuwa na ’yan mata a faɗin Nijeriya, inda ya kuma nuna yadda matsalar ta bambanta daga yanki zuwa yanki.

A cewar rahoton, binciken ya nuna cewa kusan kashi 32 cikin 100 na ’yan mata masu shekaru tsakanin 15 zuwa 19 a jihar Kebbi sun taɓa ɗaukar ciki, yayin da jihohin Zamfara da Kaduna ke biye da kashi 30 cikin 100 kowacce. A gefe guda kuma, jihohin Legas da Edo sun nuna ƙananan alƙaluma, inda kusan kashi uku cikin 100 ne kawai aka samu.

Sakamakon binciken ya samo asali ne daga Binciken ƙididdiga Kan Yawan Jama’a da Lafiya a Nijeriya na 2024 (NDHS), wanda ya bayyana bambance-bambancen da ke tsakanin yankuna tare da jaddada buƙatar zaukar matakai na musamman domin inganta lafiyar haihuwa ta ’yan mata a sassa daban-daban na ƙasar.

Rahoton ya kuma yi gargaɗin cewa ɗaukar ciki a ƙuruciya na ƙara haɗarin kamuwa da matsalolin lafiya ga uwa da jariri, har ma yana iya janyo mutuwar uwa ko jariri.

Bugu da ƙari, matsalar na haifar da ƙalubale na zamantakewa, musamman barin makaranta da ’yan mata ke yi a jihohin da matsalar ta fi tsanani.

Sai dai rahoton ya nuna cewa ilimi na taka muhimmiyar rawa wajen rage wannan matsala. A cewarsa, kashi 34 cikin 100 na ’yan mata marasa ilimi ne ke fuskantar ɗaukar ciki da wuri, yayin da wannan adadi ke raguwa zuwa kashi huɗu cikin 100 kacal ga waɗanda suka wuce matakin sakandare a karatu. Wannan na nuna cewa ilimi na taimakawa matuƙa wajen kare matasa daga irin wannan matsala.

Rahoton ya kuma bayyana cewa a shekarar 2025 ɓangaren kiwon lafiya ya faɗaɗa shirye-shiryen da suka shafi matasa domin inganta lafiyar haihuwa da kuma cika burin Shirin Samun Ingantacciyar Kula da Lafiya Ga Kowa (UHC). Wannan ya haɗa da ƙarfafa cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko da kuma shirye-shiryen wayar da kan al’umma a faɗin ƙasar.

Haka kuma an zuba jari wajen samar da ayyukan kiwon lafiya da suka dace da matasa a cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko, ciki har da ba da shawarwari kan tazarar haihuwa, rigakafin cutar ƙanjamau, da kuma kula da cututtukan da ake kamuwa da su ta hanyar jima’i.

Rahoton ya kuma nuna cewa an tura ma’aikatan lafiya na al’umma zuwa yankuna daban-daban domin ba matasa shawarwari da wasu ayyukan tsara iyali, musamman a yankunan karkara da ke da nisa daga cibiyoyin lafiya, domin su samu bayanai da kulawar da suke buƙata.

Bugu da ƙari, an ƙarfafa shirye-shiryen tsafta da kula da muhalli a makarantu da al’umma, musamman na ruwa, tsafta da muhalli (WASH), domin inganta lafiyar matasa da rage kamuwa da cututtuka masu yaɗuwa.

Rahoton ya kuma nuna ci gaba a ɓangaren kula da tsaftar jinin al’ada, inda kashi 95 cikin 100 na ’yan mata suka bayyana cewa suna da damar wanke jikinsu da canza kayan al’ada cikin sirri a gidajensu, yayin da kashi 94 cikin 100 ke amfani da kayan da suka dace a lokacin al’ada.

By ukarofi