Nijeriya ta fice daga tsananin matsin tattalin arziki – Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ƙasar ta fara fita daga mawuyacin halin tattalin arzikin da ta shiga a baya, yana mai cewa a halin yanzu gwamnoni a jihohin ƙasar ba sa sake komawa bankuna domin karɓar bashi don biyan albashin ma’aikata.

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin addinai da sarakunan gargajiya domin buɗa-baki na haɗin gwiwar addinai a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja.

Bayanin hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabarun Hulɗa da Jama’a, Bayo Onanuga, ya fitar.

Yayin da yake jawabi a wajen taron, Shugaba Tinubu ya nuna godiya ga Allah da kuma al’ummar Nijeriya bisa damar da aka ba shi ta jagorantar ƙasar, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofi da za su tabbatar da bunƙasar tattalin arziƙi da walwalar al’umma.

A cewarsa, duk da irin ƙalubalen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta gada, sauye-sauyen da aka fara aiwatarwa sun fara haifar da sakamako mai kyau.

Ya ce: “Ina matuƙar godiya da aka ba ni wannan dama ta yi wa ƙasa hidima. Abin da zan iya yi kawai shi ne in tabbatar da cewa zan kasance mai aminci wajen sauke nauyin da aka ɗora min.”

Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa alamomin farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar sun fara bayyana, inda ya ce tattalin arzikin Nijeriya yana kan hanyar gyaruwa.

A cewarsa, daga cikin manyan alamomin wannan cigaba akwai yadda jihohi ba sa sake neman rancen gaggawa daga bankuna domin biyan ma’aikatansu albashi.

Ya ce: “Zan iya cewa tattalin arzikin ƙasar ya fara gyaruwa. Masu karɓar fansho ma suna fara samun sauƙi a hankali. Mun ceci Nijeriya daga faɗawa cikin durƙushewar tattalin arziki.”

Tinubu ya bayyana cewa lokacin da gwamnatinsa ta karɓi ragamar mulki, halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki ya kasance mai matuƙar wahala. Sai dai ya ce a yanzu an fara ganin hasken nasara sakamakon gyare-gyaren da ake aiwatarwa.

“Lokacin da muka karɓi mulki al’amura sun kasance masu matuƙar wahala da ƙalubale. Amma a yau ina iya cewa da alfahari cewa mun tsallake wannan mawuyacin hali,” inji shi.

A ɓangaren tsaro kuwa, Shugaban ƙasar ya jaddada cewa gwamnati ba za ta bari ƙungiyoyin ta’addanci ko wasu masu neman tayar da zaune tsaye su yi nasara ba.

Ya amince cewa har yanzu ana fuskantar wasu barazanar tsaro, amma ya ce dakarun tsaro suna ƙara ƙaimi wajen fatattakar ’yan ta’adda a sassa daban-daban na ƙasar.

Ya ce: “Haƙiƙa muna fuskantar ƙalubale, amma ’yan ta’addan suna cikin matsin lamba saboda ana ci gaba da murƙushe su. Duk da haka, Nijeriya ba za ta taɓa miƙa wuya ba.”

Shugaban ƙasar ya kuma sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari mai yawa a muhimman fannoni kamar noma da ilimi, yana mai cewa waɗannan fannoni su ne ginshiƙan ci gaban ƙasa a nan gaba.

Tinubu ya buƙaci ’yan Nijeriya su ci gaba da kasancewa masu fata da kyakkyawan zato, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnati na aiki tuƙuru domin gina ƙasa mai zaman lafiya, tsaro da ci gaban tattalin arziki.

By ukarofi