Kwastom ta kama ƙwayoyin Tramadol 248,500 masu darajar miliyan N273 a Yobe

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kwastom ta Nijeriya ta samu gagarumar nasara a yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi bayan ta kama ƙwayoyin Tramadol Hydrochloride (mai nauyin 250mg kowanne) guda 248,500, waɗanda aka kiyasta kuɗinsu a kasuwa sun kai kimanin Naira miliyan 273.35 a jihar Yobe.

Shugaban Sashen Ayyuka na Tarayya na Yanki D da ke Bauchi na Hukumar Kwastom, Kwanturola Abdullahi Ka’ila, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Litinin.

Ya ce nasarar ta samu ne sakamakon ingantaccen tattara bayanan sirri, haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, da kuma tsauraran matakan sa ido da jami’an sashen suka ɗauka domin daƙile safarar haramtattun kayayyaki.

A cewarsa, jami’an sashen sun samu sahihan bayanai cewa ana shirin shigar da wata babbar lodin kwayoyin Tramadol ta hanyoyin sirri a kauyen Gumsi da ke ƙaramar hukumar Nguru a jihar Yobe.

“Bayan samun bayanan sirrin, an tsara wani shiri na musamman tare da sanya jami’an sa ido domin bibiyar lamarin. A yayin gudanar da wannan aiki, jami’anmu sun samu nasarar kwato kwayoyin Tramadol Hydrochloride (250mg) guda 248,500, waɗanda ake kiyasta darajarsu a kasuwa ta kai Naira miliyan 273,350,000,” inji Ka’ila.

Ya ƙara da cewa, wannan aiki ya tarwatsa wata babbar ƙungiyar masu safarar kwayoyin Tramadol ba bisa ƙa’ida ba, wadda ake zargin tana da alaƙa da wasu ƙungiyoyi a ƙasashen makwabta da ma kasuwannin ƙasa da ƙasa.

Ka’ila ya bayyana cewa wanda ake zargi da safarar ƙwayoyin ya tsere zuwa cikin daji bayan ya hango motocin sintiri na jami’an kwastom.

A cewarsa, wannan nasara za ta taimaka matuƙa wajen rage yaɗuwar shan miyagun kwayoyi, musamman a tsakanin matasa da ɗalibai, domin hana irin wazannan kwayoyi shiga kasuwa cikin sauƙi.

“Ta hanyar kama irin waɗannan kayayyaki, Hukumar Kwastom ta Nijeriya tana ƙara ƙarfafa tsaron ƙasa, tare da rage kuɗaɗen da ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke samu domin gudanar da ayyukansu,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa wannan kamun zai taimaka wajen hana asarar kuɗaɗen shiga na gwamnati ta hanyar shigo da kaya ba bisa ƙa’ida ba, tare da kare kamfanonin magunguna na halal daga gasa mara adalci da kuma yaɗuwar kayayyakin jabu.

Kwanturolan ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, ciki har da Hukumar Yaƙi da Sha da Safarar Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) da kuma Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC).

Har ila yau, ya ce za su ci gaba da wayar da kan al’umma domin su riƙa sanar da hukumomi idan sun ga wasu abubuwa masu tayar da hankali a yankunansu.

Ka’ila ya gode wa Babban Kwanturolan Kwastom na Nijeriya, Bashir Adeniyi, da kuma shugabannin hukumar bisa jagoranci da goyon bayan da suke bai wa jami’an sashen wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

A ƙarshe, ya bayyana cewa wannan kamun na daga cikin muhimman nasarorin da Nijeriya ke samu a yaƙi da safarar miyagun kwayoyi, yana kuma nuna tasirin aikin tattara bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomi wajen yaƙi da ayyukan haramtattu.

Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro, shugabannin al’umma da ɗaukacin jama’a da su kasance cikin shiri da kuma bayar da haɗin kai domin kawar da matsalar safarar miyagun kwayoyi a faɗin ƙasar.

By ukarofi