Nauyin bashi na ci gaba da matsin lamba ga tattalin arzikin Nijeriya – Rahoto

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Matsin tattalin arziƙi na ci gaba da ƙara tsananta wa Nijeriya yayin da kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke kashewa wajen biyan bashin ƙasa suka zarce kuɗin da ake warewa domin ayyukan raya ƙasa da kimanin Naira tiriliyan 3.9 a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Rahoton bayani da jaridar News Point Nigeria ta samu daga Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta kashe jimillar Naira tiriliyan 27.2 wajen biyan bashi tsakanin shekarun 2024 da 2025. Wannan na nuni da yadda nauyin bashi ke ƙara danna tattalin arzikin ƙasar.

Takardar bayanin, wadda Mai Ba Ministan Kuɗi da Ministan Kula da Tattalin Arziki Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa, Dakta Ogho Okiti, ya shirya, ta bayyana cewa hauhawar kuɗin biyan bashin ya samo asali ne daga wasu manyan dalilai na tattalin arziki, musamman raunin darajar Naira da kuma hauhawar ribar lamuni a cikin gida.

Bayanan sun nuna cewa a shekarar 2024, gwamnatin tarayya ta kashe Naira tiriliyan 12.63 wajen biyan bashin ƙasa. Wannan adadi ya fi abin da aka ware a kasafin kuɗin shekarar, wanda ya kai Naira tiriliyan 8.56.

A shekarar 2025 kuwa, kuɗin biyan bashin sun ƙara tashi zuwa Naira tiriliyan 14.57, wanda shi ma ya zarce abin da aka ware a kasafin kuɗi, wato Naira tiriliyan 13.12.

Idan aka haza adadin na shekarun biyu, ya nuna cewa Nujeriya ta kashe kusan Naira tiriliyan 27.2 wajen biyan bashin ƙasa, lamarin da ke nuna ƙara tsanantar matsin tattalin arziki sakamakon hauhawar kuɗin ruwa da kuma sauye-sauyen darajar musayar kuɗi.

Rahoton ya kuma nuna cewa tsakanin shekarar 2024 da 2025, kuɗin biyan bashin sun ƙaru da Naira tiriliyan 1.94, wanda ke wakiltar ƙarin kaso 15.4 cikin ɗari.

Har ila yau, bayanan sun nuna cewa a duka shekarun biyu, ainihin kuɗin da aka kashe wajen biyan bashin sun zarce abin da aka tsara a kasafin kuɗi.

A 2024, an wuce kasafin kuɗin biyan bashin da kusan Naira tiriliyan 4.07, yayin da aka kashe Naira tiriliyan 12.63 maimakon Naira tiriliyan 8.56 da aka amince da su.

Ko da yake giɓi ya ragu kaɗan a shekarar 2025, har yanzu akwai babban bambanci, inda aka kashe Naira tiriliyan 14.57 maimakon Naira tiriliyan 13.12 da aka tanada.

A jimlace, gwamnatin tarayya ta wuce kasafin kuɗin biyan bashin da kusan Naira tiriliyan 5.52 a cikin shekarun biyu.

Ma’aikatar kuzin ta bayyana cewa hauhawar kuɗin biyan bashin ba wai saboda sabon lamuni ba ne kawai, amma saboda wasu dalilai na tattalin arziki.

Ta ce, sauyin darajar musayar kuɗi ya ƙara nauyin bashin waje da ake biya da kuɗaɗen ƙasashen waje.

“Bashin waje ana rubuta shi ne da kuɗin ƙasashen waje. Idan darajar Naira ta ragu, adadin Naira da ake buƙata wajen biyan bashin dalar Amurka zai ƙaru kai tsaye. Wannan tasirin lissafi ne, ba wai sabuwar rance ba,” inji rahoton.

By ukarofi