Annobar tsutsa na barazana ga noman tumatiri a Kano, inji manoma rani

Spread the love

Daga DAUDA USMAN

Kungiyar Manoman Rani a jihar Kano ta bayyana damuwarta kan wata annoba ta tsutsa mai suna Sharon wadda ke lalata gonakin tumatiri, lamarin da ke janyo asarar maƙudan kuɗi ga manoma a duk shekara.

Shugabannin ƙungiyar sun yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta gaggauta ɗaukar mataki domin nemo maganin da zai kawo ƙarshen wannan matsala.

Shugabannin ƙungiyar manoman rani ta ƙasa da kuma na reshen jihar Kano da ke yankin kasuwar ‘Yan Gwari ta Kwanar Gafan a ƙaramar hukumar Garun Malam ne suka bayyana haka yayin wani taron ƙungiyar da aka gudanar a Kano ranar Lahadi da ta gabata.

Taron ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a harkar noman tumatiri a faɗin jihar.

Shugaban ƙungiyar manoman rani ta jihar Kano, Alhaji Zailani Manchi, tare da shugaban ƙungiyar na yankin Kwanar Gafan, Alhaji Zailani Ibrahim, da uban ƙungiyar Alhaji Usman Mai Waya, sun bayyana cewa tsutsar Sharon na cinye shukar tumatiri tun daga lokacin da ta fara tsiro har zuwa lokacin da ‘ya’yanta suka nuna, abin da ke haddasa babbar asara ga manoma.

Taron ya kuma samu halartar mataimakin shugaban ƙungiyar Alhaji Abubakar Sha’aibu da sakataren ƙungiyar Alhaji Hashimu Zato, da shugaban ƙungiyar masu saye da sayar da kayan miya Alhaji Labiru Abdullahi, da kuma wasu dattawan kasuwa da masu ruwa da tsaki a harkar tumatiri.

A jawabansu daban-daban, shugabannin ƙungiyar sun tattauna hanyoyin da za su bi domin shawo kan matsalar, tare da musayar shawarwari kan yadda za a nemo maganin feshi da zai iya kashe tsutsar. Sun ce duk shekara manoma na ƙoƙarin samun irin wannan magani amma har yanzu ba a samu wanda zai kawo cikakkiyar mafita ba.

Shugaban ƙungiyar na jihar Kano, Alhaji Zailani Manchi, ya ce manoma na fuskantar babbar matsala saboda tsutsar Sharon na lalata amfanin gonar tumatiri gaba ɗaya. Ya ce saboda haka ne ƙungiyar ke kira ga gwamnatin jihar Kano da ta taimaka wajen gudanar da bincike domin gano ingantaccen magani, ko da kuwa daga wasashen waje ne da suka yi fice wajen noman tumatiri da sauran kayan miya.

Sauran shugabannin da suka yi magana a taron sun jaddada wannan kira, suna mai cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, matsalar na iya kara tsananta, lamarin da zai shafi samar da tumatiri a jihar Kano da ma kasa baki ɗaya.

A nasa ɓangaren, uban ƙungiyar, Alhaji Usman Mai Waya, ya bayyana cewa idan gwamnati ta taimaka ta samar da maganin kashe tsutsar Sharon, jihar Kano za ta iya samar da tumatiri da zai wadatar da Nijeriya baki ɗaya, har ma a rika kai wa ƙasashen makwabta. Ya ce hakan zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin manoma da kuma samar da wadataccen kayan miya ga al’umma.

By ukarofi