Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Ci Gaban Shiya ta aike da takardar koke ga Hukumar Kare Haƙƙin ɗan Adama (NHRC) a Abuja, tana neman shiga tsakani kan yadda aka gudanar da zaben sarautar Shiya da ta ce bai bai wa zaɓin jama’a adalci ba.
A cikin takardar koken da ƙungiyar ta rubuta, ta bayyana cewa al’ummar Shiya da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Baruten a jihar Kwara sun fara tsarin zaɓen sabon shugaban gargajiya ne bayan samuwar gibi a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2024. Sai dai ƙungiyar ta ce tsarin ya kasance cike da kura-kurai, nuna ɓangaranci da kuma tsoma bakin wasu ɓangarori daga waje.
Takardar ta bayyana cewa masarautar Shiya na ƙarƙashin majalisar masarautar Okuta, wadda ke da Sarkin Okuta a matsayin ɗaya daga cikin manyan hukumomin gargajiya. Duk da haka, ƙungiyar ta ce al’ummar Shiya sun yi mamaki matuƙa lokacin da wanda suka fi so a matsayin sarki bai samu nasara ba a sakamakon da aka sanar.
Kungiyar ta yi zargin cewa an samu matsala a tsarin kammala zaɓen, inda ta ce lamarin ya nuna ɓangaranci da wasu muradun da ba su dace ba, abin da ya kusa janyo rikici a cikin al’umma.
Ta kuma ce bayan sanar da sakamakon, an samu barazana da kama wasu mutane da jami’an ‘yan sanda suka yi kan waɗanda suka nuna rashin amincewa da abin da ya faru.
A cewar ƙungiyar, al’ummar Shiya mutane ne masu son zaman lafiya, kuma sun ci gaba da nuna haƙuri tun bayan faruwar lamarin. Ta ce an yi ƙoƙarin ganin an ba wanda jama’a suka fi so sarautar, amma duk ƙoƙarin bai haifar da sakamako ba.
Kungiyar ta bayyana cewa sarautar gargajiya a Shiya tana da matuƙar muhimmanci kuma ana girmama ta sosai a tsakanin al’umma. Ta kuma ce a halin yanzu al’ummar yankin na rayuwa cikin fargaba saboda tsoron hare-hare daga ɓangaren wanda aka naɗa a matsayin shugaban gargajiya, wanda a cewarsu an naɗa shi ba bisa ra’ayin jama’a ba.
Saboda haka, ƙungiyar ta roƙi Hukumar Kare Haƙƙin ɗan Adam ta kasa da ta shiga tsakani cikin gaggawa domin magance matsalar, tare da taimakawa wajen tabbatar da cewa an dawo da adalci a zaben sarautar.
Kungiyar ta bayyana fatan cewa hukuma za ta dauki mataki cikin lokaci domin kawo ƙarshen rikicin da kuma tabbatar da cewa zaɓin da jama’a suka amince da shi shi ne ya hau kujerar sarautar.
