Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar ƙarfafa Matasan Arewa da Wayar Musu da Kai, wato Northern Youth Empowerment & Enlightenment Forum (NYEEF), ta fitar da wata muhimmiyar sanarwar manufofi bayan kammala Taron Tattaunawa na Shekara karo na uku da ta gudanar a watan Janairun 2026 a jihar Kaduna.
Taron, wanda aka shirya domin karrama marigayi Alhaji Suleiman Abubakar Uban Doman Gudu, tsohon Daraktan Harkokin Sarauta na ƙungiyar, ya haɗa manyan malamai, shugabannin addini, kwararrun harkokin tsaro, masu tsara manufofi, shugabannin matasa da kuma ‘yan jarida domin nazarin manyan matsalolin da ke addabar Arewacin Nijeriya da ma kasa baki ɗaya.
A sanarwar da Sakataren Kwamitin Tsaro na ƙungiyar, Kwamaret Salihu Dantata ya sanyawa hannu, mahalarta taron sun fara ne da jinjinawa rayuwar marigayin, inda suka bayyana shi a matsayin jagora mai gaskiya, kishin ƙasa da kuma jajircewa wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Sun jaddada aniyar ci gaba da tafiya a kan tafarkin da ya bari na haɗin kai, adalci da shugabanci nagari.
Batun tsaro ya mamaye muhawarar taron, inda aka bayyana rashin tsaro a matsayin babbar barazana ga zaman lafiyar al’umma da tattalin arzikin Arewacin Nijeriya. Mahalarta taron sun nuna damuwa kan yadda ayyukan ‘yan bindiga, sace-sacen mutane, ta’addanci, rikicin manoma da makiyaya da kuma rikice-rikicen ƙabilanci suka janyo raguwar noma, tarwatsa al’umma daga gidajensu, lalata kadarori da ababen more rayuwa, da kuma ƙaruwar marasa aikin yi tare da tsanantar matsalar jinƙai.
Sun yi ittifaƙi cewa ya kamata a ɗauki matsalar tsaro a matsayin matsalar gaggawa ta tattalin arziki a matakin ƙasa, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na tarayya, jihohi da kuma al’umma. Haka kuma sun jaddada muhimmiyar rawar da sarakuna da sauran hukumomin gargajiya za su iya takawa wajen tattara bayanan sirri da daƙile rikice-rikice tun kafin su balle.
A ɓangaren noma da wadatar abinci, taron ya lura cewa rashin samun damar zuwa gonaki sakamakon matsalolin tsaro ya rage yawan abincin da ake nomawa, abin da ke ƙara jefa al’umma cikin matsin rayuwa. Mahalarta taron sun buƙaci gaggawar ɗaukar matakan tsaro a yankunan karkara domin bai wa manoma damar komawa gonakinsu.
Matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa ita ma ta samu kulawa ta musamman. An bayyana cewa ƙaruwar rashin aikin yi na jefa matasa cikin haɗarin faɗawa aikata laifuka da sauran miyagun ɗabi’u.
Taron ya amince cewa samar da ayyukan yi, horas da matasa sana’o’i da kuma faɗaɗa damar tattalin arziki su ne muhimman hanyoyin da za su taimaka wajen rage talauci da hana matasa faɗawa hannun masu tada zaune tsaye.
