Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kamfanin Saka Hunnun Jari ya bayyana cewa, Bankunan Ajiyar Kuɗi na Nijeriya (DMB) sun tara Naira Tiriliyan 2.8 daga Cibiyar Bada Lamuni ta Babban Bankin Nijeriya (CBN) don rufe giɓin kuɗaɗen ɓudanar da ayyukansu.
Masu ba da lamuni na cikin gida sun yi ta tururuwa a cibiyar bayar da lamuni na CBN don rancen kuɗaɗe don biyan buƙatunsu na yau da kullum.
“Adadin da ke cikin tsarin hada-hadar kuɗi ya ƙaru sosai yayin da kuɗaɗen shiga daga ‘FGN bond coupon’ da ya kai Naira biliyan 402.96 ya cika tsarin,” inji Cordros Capital Limited.
“A mafi yawan lokuta, yawan kudin da ake samu ba ya da kaiwa, inda akasarin bankuna ke dogaro da Babban Bankin CBN na bayar da lamuni na gudanar da ayyukansu,” inji AIICO Capital Limited.
Sakamakon lamuni da bankunan kasuwanci suka samu, yawan kuɗin da ake samu a kasuwannin hada-hadar kuɗi ya ƙaru da kashi 62.4 cikin 100 a makon nan inda aka rufe kan Naira tiriliyan 1.2, inji Afrinɓest Limited a cikin wata sanarwa.
