Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya roƙi ‘yan Nijeriya da su ƙara haƙuri kan wahalhalun da suke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur da sauran sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta ɓullo da shi, yana mai cewa nan ba da daɗewa ba za su fara cin gajiyar waɗannan manufofi.
Shugaban ya yi magana ne a ranar Litinin a taron shekara-shekara na Cibiyar Gudanarwa ta Nijeriya (NIM) na shekara ta 2024 da aka gudanar a Fatakwal, Jihar Ribas.
Shugaban Ma’aikata na Tarayya Didi Esther Walson-Jack ta wakilci Tinubu, wanda shi ne babban baƙo na musamman a wajen taron, ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin daidaita tattalin arzikin da ya gada.
Ya ce a cikin ƙanƙanin lokacin da ya shafe yana tafiyar da harkokin ƙasar, gwamnatinsa ta samu ci gaba mai ma’ana wajen hacaka tattalin arziki, tare da zuba jari sosai a wasu sassa masu muhimmanci, kamar noma, fasaha, da lantarki.
Ya ci gaba da cewa, “A ƙoƙarin da muke na gaggauta fara aiki da daidaita tattalin arzikin da muka gada, mun ɗauki wasu matakai masu tsauri ta hanyar sauye-sauyen tattalin arziki da aka ɓullo da su kawo yanzu kamar batun haɓaka Naira da kuma cire tallafin man fetur.
“Mun fahimci cewa raɗaɗin da waɗannan manufofin tattalin arziki na kawo sauyi ke ci wa ‘yan ƙasa tuwo a kwarya amma muna da yaƙinin cewa tattalin arzikin ƙasa da ‘yan Nijeriya za su fara cin gajiyar dukkan manufofi nan da wani lokaci kaɗan.”
