Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Rundunar sojojiin Nijeriya ta sallami wata soja mai suna Priɓate Ruth Ogunleye daga aiki bayan da ta zargi wani babban jami’in soja, Kanar I.B Abdulkareem da neman yin lalata da ita.
Sojar ta yi wannan zargin ne ta hanyar asusunta na TikTok a watan Janairun 2024, inda ta ce Abdulkareem tare da wasu manyan jami’ai sun tursasa ta tare da tilasta mata shiga asibitin masu taɓin hankali bayan ta ƙi amincewa da buƙatarsu.
Da yake amsa waɗannan zarge-zargen, babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya bayar da umarnin gudanar da bincike.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Talata, Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana cewa bayan kammala nazari na gaskiya, da shaidu, da kuma shaidun da aka gabatar, an tabbatar da cewa Abdulkareem bai aikata laifukan da Ogunleye ke zarginsa ba.
Onyema ya kuma bayyana cewa, tun shekarar 2022 aka ba Ogunleye shawarar a sallame ta bisa dalilai na lafiya, amma rundunar sojojin Nijeriya ta nuna juyayinta, ta samar mata da mafi kyawun magani kafin a sallame ta cikin rayuwar farar hula.
Sojar da rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya ta yi wa ritaya saboda rashin lafiya bayan ta zargi wasu manyan hafsoshi da cin zarafinta ta sake magantuwa.
A watan Janairu ne Ruth Ogunleye ta fito a shafinta na TikTok tana cewa ta sha wahala sanadiyar wasu manyan hafsoshin sojin rundunar.
Zargin nata ya haifar da cecekuce a lokacin, inda ministar mata ta shiga maganar, har ta zanta da babban hafsan soji a lokacin.
Bayan sanar da yi mata ritayar ce Ms Ogunleye ta sake fitowa a wani bidiyon a TikTok, inda ta ce tana so a wallafa sakamakon binciken a duka kafofin sada zumunta domin kowa ya gani.
“A ranar 9 ga Janairun 2024, na fito a kafofin sadarwa na yi ƙorafin cin zarafi da fyaɗen da aka yi mani. Da yadda aka nuna ni da bindiga, aka saka mani ankwa, aka ajiye ni a wani ofis na kwanaki. Ina roƙon rundunar sojin Nijeriya ta bayyana sakamakon binciken da ta yi kowa ya gani,” inji ta.
A ranar Talata ne Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana sakamakon binciken, inda ya ce sun gano wanda take zargi Kanal I.B. Abdulkareem bai aikata laifin ba, sannan ya ƙara da cewa an yanke shawarar yi mata ritaya ne domin rashin lafiya bayan ta ƙi amincewa a duba lafiyarta.
