Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Sufeto Janar na ’yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya bai wa rundunar ‘yan sandan Nijeriya umarnin ci gaba da bayar da takardar izinin baƙin gilashin mota ‘tinted glass’ a faɗin ƙasar.
Muyiwa Adejobi, kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce matakin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da jama’a ke yi game da yadda ake muzguna wa masu ababen hawa masu baƙin gilashin mota.
Ya ce, shirin ya nuna buƙatar da ake da ita na samar da tsari mai tsafta, mai gaskiya da sanin yakamata domin daidaita tsarin baƙin gilashin mota.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Akwai buƙatar a samar wa motocin zamani da ke zuwa da baƙin gilash tsarin da ya dace don tabbatar da tsaron jama’a,” inji sanarwar.
Adejobi ya ce sake dawo da tsarin bayar da izinin wani shiri ne na gano masu amfani da doka, kamar mutanen da ke da buƙatun likita ko kuma jami’an tsaro, tare da hana yin amfani da su wajen aikata laifuka.
Ya ce ana sa ran za a ƙara ƙarfin binciken ‘yan sanda da kuma ƙarfafa ayyukan tsaron ƙasa.
Yadda ake samun izinin gilashin tint a Nijeriya ba tare da zuwa ofishin ’yan sanda ba:
Bisa ga shawarar ‘yan sanda, tsarin ya ƙunshi abubuwa kamar haka:
1. Ana buƙatar masu neman izini su ziyarci tashar yanar gizo ta ‘yan sanda ta ‘Specialized Serɓices Automation Project’ a shafin www.possap.gov.ng kuma su yi rajista ta amfani da Lambar Shaida ta ƙasa (NIN), Lambar Shaidar Banki ta BɓN, ko Lambar Shaida ta Biyan Haraji.
2. Bayan cika fom ɗin rajista tare da cikakkun bayanan sirri, masu amfani dole ne su ƙirƙira asusu kuma su tabbatar da shi ta amfani da lambar da aka aika zuwa imel ɗin su.
3. Da zarar an tabbatar, za su iya shiga ta amfani da imel da kalmar sirri don ci gaba da ragista.
4. Masu nema dole ne su zaɓi tsarin “Tinted Glass Permit”, su shigar da bayanan abin hawa, sannan a loda duk takardu masu muhimmanci.
5. Bayan tabbatar da duk bayanan, ana sa ran za su biya kuɗin da ake buƙata. Bayan duk waɗannan, za su jira na ɗan wani lokaci kafin a tabbatar da su.
