Gwamnatin Borno ta dakatar da kansila kan zargin cin mutunci

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA A abuja

Gwamnatin Jihar Borno ta dakatar da kansila mai wakiltar Yawa Kura a ƙaramar Hukumar Abadam, Mele Mohammed, bisa zarginsa da aikata ba daidai ba a shafukan sada zumunta.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda a hukumance mai ɗauke da sa hannun Bashir Goni Sanda, muƙaddashin daraktan harkokin ƙananan hukumomi a madadin Kwamishina, kamar yadda Manhaja ta samu.

Dakatarwar ta biyo bayan rashin mutunta Shugaban ƙaramar Hukumar Abadam, Malam Fatori da Mohammed ya yi ta kafafen sada zumunta na zamani – matakin da aka bayyana a matsayin saɓa dokokin da ake da su na gudanar da ayyukan jami’an gwamnati.

Wasiƙar wacce kuma aka yi kwafinta zuwa ga Shugaban Hukumar ta bayyana cewa dakatarwar za ta ci gaba da aiki har sai an ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Bashir ya ƙara da cewa, matakin da Mohammed ya ɗauka bai dace da mutumin da ke riƙe da irin wannan babban muƙami na gwamnati ba, ya kuma ce gwamnati na kallon lamarin a matsayin babban karya doka da kuma bin diddigin al’amura.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “An umurce ni da in rubuta kuma in duba batun da ke sama da kuma bayar da amincewar dakatar da kai daga muƙamin kansilan Yawa Kura a ƙaramar Hukumar Abadam har sai an yanke hukunci.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Dakatarwar ta zama dole ne sakamakon rashin ɗa’a na wanda ke riƙe da irin wannan matsayi na rashin mutunta shugaban ƙaramar hukumar ta kafafen sada zumunta wanda ya saɓawa doka.”

By ukarofi