Yadda Ganduje ya yi murabus daga muƙaminsa cikin girma, inji APC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jam’iyyar APC ta yi magana game da murabus zin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje.

APC ta tabbatar da murabus ɗin Ganduje ta wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Feliɗ Morka, ya fitar a ranar Juma’a, 27 ga watan Yuni, 2025.

Morka ya bayyana cewa murabus ɗin Ganduje, wanda ya ba shi damar halartar al’amuran cikin gaggawa da muhimmanci, ya fara aiki nan take.

Wasiƙar murabus ɗin Ganduje, wacce ya miƙa tun a ranar Juma’a, an miƙa wa kwamitin ayyuka na jam’iyyar na ƙasa (NWC), ta hannun sakataren jam’iyyar na ƙasa, Ajibola Basiru.

Morka ya ce, an umurci mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa (Arewa), Ali Dalori da ya karɓi muƙamin shugaban riƙo na ƙasa, har zuwa lokacin da za a gudanar da taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) a watan Disamba.

Wannan, inji shi, an yi gaggawar cike gurbin da Ganduje ya bari.

Morka ya ce: “A tsawon wa’adinsa, ya sadaukar da kansa wajen ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar, da bayyana manufofinta na dimokuraɗiyya da kuma ƙara ƙarfin jam’iyyar a zaɓuka.

“Amincewar da hukumar zaɓe ta jam’iyyar ta ƙasa da kuma taron shugabannin jam’iyyar na ƙasa suka ba shi a watan Fabrairun 2025 ya kasance babban karramawa da girmamawa ga hidimarsa.

“Ya bar muƙaminsa na shugaban jami’iyyar na ƙasa tare da alfahari da nasarorin da muka samu tare, ciki har da shigowar ‘yan jam’iyyun adawa da kuma tabbatar da halascin shugabancin jam’iyyarmu.”

Ya kuma tabbatar wa jam’iyyar APC masu aminci cewa jam’iyyar ta ci gaba da tsayawa tsayin daka a kan manufofinta na ganin an kawo sauyi ga ‘yan Nijeriya baki ɗaya, kamar yadda ƙudirin Shugaban ƙasa Bola Tinubu na Renewed Hope ya buƙata.

Kakakin jam’iyyar APC ya nuna jin daɗinsa ga Ganduje bisa irin gudunmawar da ya bayar da kuma tarihin hidimar jam’iyyar.

Ya yi addu’ar Allah ya ba shi lafiya, ya kuma ba shi nasara a ayyukan sa na rayuwa da kuma yi wa ƙasa da bil’adama hidima.

Mutane dai sun yi zargin ruwa ba ya tsami banza, ko kuma dai da walakin goro a miya amma uwar jam’iyyar ta yi watsi da wannan hasashe.

Daraktan yaɗa labarai na jam’iyyar ta APC, Bala Ibrahim, ya shaida cewa babban dalilin da Ganduje ya bayar a game da murabus ɗin na sa shi ne batun kiwon lafiya.

Ya ce,” Ganduje ya nemi a amince ya sauka daga muƙamin shugaban jam’iyya saboda ya mayar da hankali wajen kula da lafiyarsa.”

Bala Ibrahim, ya ce, Duk mutumin da ya haura shekara 70 dole ne ya yi taka-tsan-tsan domin kula da lafiyarsa domin ganin cewa tafiya ta yi kyau.”

“Shugaban ƙasa ya amince da murabus ɗin na Ganduje haka suma ‘yan kwamitin gudanarwa na jam’iyya suma sun amince, kai kowa dai ya amince da cewa matakin na Ganduje ya yi daidai ya je ya kula da lafiyarsa yayin da ita kuma jam’iyya za ta mayar da hankali wajen yin abubuwan da za su ƙara ƙarfafata da samun nasara a zaɓukan da ke tafe,” inji shi.

Bala Ibrahim ya ce, zargin da ake cewa ruwa ba ya tsami banza, ko kuma dai da walakin goro a miya a game da murabus ɗin na Ganduje, duk ba gaskiya bane.

Ya ce,” Duk abin da ba a tabbatar da shi ba haka kuma bincike ma bai tabbatar da shi ba to zato ne kuma zato zunubi ne ko da ya tabbata.”

Daraktan yaɗa labaran jam’iyyar ta APC, ya ce “Game da batun wanda zai maye gurbin shugaban jam’iyyar da Sauka, dama jam’iyya na da kundin tsarin mulki wanda ya yi tanadi irin wannan wanda idan shugaban jam’iyya ya sauka daga muƙaminsa to za a zaɓi ɗaya daga cikin muƙaddansa biyu wanda ɗaya daga Arewa ɗaya kuma daga Kudu to sai a bai wa wanda ya fito daga yankin da shugaban da ya yi murabus ya fito a bashi riƙon ƙwarya kafin a gudanar da zaɓen wanda zai gaji kujerar.”

Ya ce,” A wannan hali muƙaddashi na arewa tun da Ganduje daga shiyyar ya fito wanda shi ne Bukar Dalori, shi ne zai riƙe kujerar na wucin gadi har lokacin da aka zaɓi sabon shugaban jam’iyyar.”

A watan Agustan 2023 ne Ganduje ya karɓi ragamar shugabancin jam’iyyar APC, bayan murabus ɗin da magabacinsa Abdullahi Adamu ya yi.

By ukarofi