Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta miƙa ɗan wasanta Ansu Fati a matsayin aro ga takwararta Monaco da ke gasar Ligue 1 ta Faransa.
Da wannan mataki, Ansu Fati ya zama can wasa na uku da ƙungiyar Monaco ta ƙulla yarjejeniya da shi gabanin fara sabuwar kakar wasa.
A baya bayan nan ne dai ƙungiyar ta ɗauko mai tsaron baya na tawagar ƙwallon ƙafar Ingila Eric Dier daga Bayern Munich, sai kuma can wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba, wanda ya shafe watanni ba tare da ƙungiya ba, saboda haramcin buga wasannin watanni 18 da ya kammala aiki kansa, saboda samunsa da aka yi da laifin shan haramtattun ƙwayoyin ƙarin kuzari a lokacin da ya koma taka wa Juventus leda bayan rabuwarsa da Manchester United.
A ranar Alhamis 3 ga watan Yulin da muke ƙungiyar Monaco za ta gabatar da dukkanin sabbin ’yan wasan ga magiya bayanta.
