Yadda jigon APC ya rasu bayan faɗa wa ramin lifta a otel ɗin Abuja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Barista Abdulsalami Ginsau, ya rasu da safiyar ranar Juma’a bayan wani mummunan hatsari da ya faru a wani otel da ke yankin Utako a birnin Abuja.

Marigayin, wanda aka zaɓa kwanan nan a matsayin Mataimakin Sakataren Tsare-tsare na jam’iyyar a Kano, ya gamu da ajalinsa ne bayan faɗawa cikin ramin lif (eleɓator shaft) na otel ɗin, lamarin da ya girgiza mahalarta taron jam’iyyar da mazauna yankin.

Bincike ya nuna cewa ba kamar yadda aka fara yaɗawa ba cewa ya maƙale a cikin lif, sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa lif ɗin ya lalace ne tun da farko sakamakon cunkoson wakilan jam’iyya da suka halarci babban taron ƙasa na APC a Abuja. Ana zargin wasu daga cikin wakilan sun yi amfani da lif ɗin ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ya jawo matsalar aiki a cikinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa Ginsau, wanda yake sauka a bene na uku na otel ɗin, ya fito daga ɗakinsa da misalin ƙarfe 6:30 na safe, inda ya nufi lif ba tare da sanin cewa ya lalace ba. A lokacin, lif ɗin yana a wani bene daban, wanda ya bar ramin a buɗe, kuma hakan ya sa ya faɗa ciki kai tsaye.

Wata majiya daga ɓangaren tsaro ta bayyana cewa da akwai yiwuwar a ceci rayuwarsa idan wasu mutane biyu da suka ga yadda ya faɗa sun yi gaggawar sanar da ma’aikatan otel ɗin. Sai dai abin takaici, sun bar wurin ba tare da ɗaukar matakin gaggawa ba.

Majiyar ta ƙara da cewa cunkoson jama’a da rashin bin ƙa’idoji daga wasu mahalarta taron jam’iyyar ne suka haddasa matsalar, inda aka ce ɗakuna kusan 150 aka tanada, amma mutane fiye da 2,000 suka mamaye otel ɗin. Haka kuma, lif ɗin da aka tsara ya ɗauki mutum shida zuwa takwas, ana cunkusa mutane har 12 zuwa 14 a lokaci guda.

Wata babbar ma’aikaciyar otel ɗin ta nuna alhini kan faruwar lamarin, tana mai cewa ba a sanar da su cikin gaggawa ba bayan aukuwar hatsarin. Ta kuma tabbatar da cewa otel din na aiki tare da jami’an tsaro domin gudanar da cikakken bincike.

An ruwaito cewa an kai rahoton lamarin ga rundunar ‘yan sanda ta yankin Utako da kuma ta Babban Birnin Tarayya, inda suka gudanar da binciken kwararru kafin ɗaukar gawar marigayin.

Wannan lamari ya sake jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin tsaro a wuraren taruwar jama’a, musamman a manyan otel-otel, domin kauce wa irin waɗannan munanan haɗurra a nan gaba.

By ukarofi