Tsarin bankin Musulunci na ƙara samun karɓuwa a Nijeriya, inji hukumar SEC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Kula da Kasuwar Hada-hadar Jari ta ƙasa (SEC), Alhaji Aliyu Katuka, ya bayyana cewa tsarin bankin Musulunci, wato tsarin banki mara ruwa, na ƙara samun karɓuwa a Nijeriya, sakamakon wayar da kan jama’a da kuma fa’idojin tattalin arziki da yake haifarwa.

Katuka ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), a gefen taron ranar Rukunin Bankin Raya Musulunci (IsDB) da aka gudanar a birnin Legas.

Ya ce ƙaruwar amincewar masu zuba jari a kasuwar hada-hadar jari na ƙara ƙarfafa ingancin kasuwa, tare da taimakawa burin Nijeriya na gina tattalin arziki mai darajar dala tiriliyan guda.

A cewarsa, tsarin bankin Musulunci, wanda ake kira banki mara ruwa ko tsarin da ya dace da shari’ar Musulunci, yana samun karɓuwa a hankali a tsakanin ’yan Nijeriya, ba tare da la’akari da bambancin addini ba.

Ya bayyana cewa a baya, yawancin waɗanda ba Musulmi ba ba su da cikakken fahimta game da wannan tsari, abin da ya janyo jinkirin karɓuwarsa. Sai dai ya ce ƙoƙarin wayar da kai da ake yi a halin yanzu na taimakawa wajen ƙara fahimta da kuma yarda da tsarin.

Katuka ya ƙara da cewa, masu amfani da kayayyakin bankin Musulunci na jin daɗin fa’idojinsa, musamman wajen samar da ayyukan yi, bunƙasa gine-ginen more rayuwa, da kuma tallafa wa fannin ilimi da kiwon lafiya.

Ya jaddada cewa duk da cewa wannan ɓangaren na banki bai kai girman bankunan gargajiya ba tukuna, amma yana ci gaba da bunƙasa cikin sauri, tare da nuna alamun ƙarfi a nan gaba.

“Bankin mara ruwa har yanzu yana kan hanyar bunƙasa, don haka kwatanta shi kai tsaye da bankunan gargajiya ba zai nuna cikakken ƙarfinsa ba, amma yadda yake girma abin ƙarfafa gwiwa ne,” inji shi.

Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa tsarin ya dace da manufofin shigar da jama’a cikin harkokin kuɗi a Nijeriya, domin yana samar da sabbin hanyoyin samun kuɗaɗe ga waɗanda ba su da sauƙin samun damar banki.

Ya yi kira da a ƙara ƙarfafa shirye-shiryen wayar da kai domin ƙara fahimtar jama’a da kuma bunƙasa karɓuwar tsarin a faɗin ƙasar.

“Ya kamata a mai da hankali kan amfanin da tsarin ke da shi ga al’umma gaba ɗaya, ba wai bambancin addini ba. Wannan batu ne na bunƙasar tattalin arziki da walwalar kowa da kowa,” inji shi.

A ƙarshe, Katuka ya nuna kyakkyawan fata cewa ƙarin shiga cikin tsarin bankin mara ruwa zai ƙara taimakawa wajen haɓakar tattalin arziki da ci gaban Nijeriya.

By ukarofi