Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jihohin Nijeriya sun kashe jimillar Naira Biliyan 455.38 wajen biyan bashin waje a shekarar 2025, abin da ya nuna ƙarin biliyan N93.30 idan aka kwatanta da biliyan N362.08 da aka biya a 2024, kamar yadda bayanan Rabon Asusun Tarayya da Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) suka nuna.
Wannan ƙarin da ya kai kashi 25.77 cikin ɗari ya ƙara nuna yadda nauyin biyan basussuka ke ƙara takura wa kasafin jihohi, inda ake cire kuɗaɗen kai tsaye daga rabon FAAC kafin su isa hannun gwamnatocin jihohi.
Binciken ya nuna cewa daga watan Janairu zuwa Yuli 2025, an riƙa cire kusan biliyan N39 a kowane wata. A watan Agusta ne aka samu sauƙi zuwa biliyan N36.14, wanda ya ci gaba har zuwa ƙarshen shekara. Wannan ya bambanta da yanayin 2024 da aka samu canje-canje masu tsanani a watanni daban-daban.
Jihohi goma ne suka ɗauki kusan kashi 68.57 cikin ɗari na dukkan kuɗin da aka cire a 2025.
Legas ce ta fi kowa, inda aka cire mata biliyan N92.80, wanda ya kai sama da kashi 20 cikin ɗari na dukkan bashin da jihohi suka biya. Ribas ta zo na biyu da biliyan N48.58, fiye da ninki biyu na abin da ta biya a 2024. Kaduna ta bi sahu da biliyan N47.93.
Sauran jihohin da suka fito a gaba sun haɗa da Ogun da biliyan N25.20, Kuros Riba da biliyan N21.01, Oyo da biliyan N20.17, Edo da biliyan N18.70, Bauchi da biliyan N16.85, Kano da biliyan N10.63, yayin da Ebonyi ta biya biliyan N10.37.
A ɓangaren yankuna, Kudu maso Yamma ta fi kowa da biliyan N162.77, wato kashi 35.74 cikin ɗari na jimillar kuɗin. Kudu maso Kudu ta biyo baya da biliyan N100.37, sai Arewa maso Yamma da biliyan N81.97. Arewa maso Gabas ta biya biliyan N42.42, Kudu maso Gabas biliyan N40.20, yayin da Arewa ta Tsakiya ta zo aarshe da biliyan N27.65.
Ana cire waɗannan kuɗaɗe ne bisa tsarin “first-line charge” na FAAC, wanda ke bai wa biyan bashi fifiko kafin jihohi su karɓi rabonsu. Duk da cewa hakan na taimakawa wajen kare mutuncin Nijeriya a idon masu ba da lamuni, yana rage wa jihohi kuɗin da za su yi amfani da su wajen albashi, gine-gine da sauran ayyukan yau da kullum.
Hukumar NEITI ta yi gargadin cewa wasu jihohin da ke da yawan basussuka ba su cikin manyan jihohin da ke samun rabon FAAC mai yawa, lamarin da ke jefa su cikin haɗarin rashin daidaiton kuɗi.
Masana tattalin arziki sun shawarci jihohi da su rage dogaro da aro, su faɗaɗa hanyoyin ƙara kuɗaɗen shiga na cikin gida, da kuma amfani da hanyoyin lamuni masu ɗorewa domin kauce wa tsanantar matsin tattali a nan gaba.
