Farfesan jami’ar sojoji ya rasu bayan shekara guda a hannun Boko Haram

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMMAD

Wani farfesa a Jami’ar Sojin Nijeriya da ke Biu a Jihar Borno ya rasu bayan kusan shekara guda yana tsare a hannun mayaƙan Boko Haram, bayan an sace shi a kan hanyar Damaturu zuwa Biu.

Marigayi Farfesa Abubakar Mohammed El-Jummah an ruwaito cewa an yi garkuwa da shi ne a ranar 2 ga Maris, 2025, yayin da yake tafiya a kan titin Damaturu–Biu, wata hanya da ta daɗe tana fama da hare-haren ‘yan tada ƙayar baya da sace-sacen mutane a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.

Iyalan marigayin sun tabbatar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba, 11 ga Fabrairu, 2026, inda suka bayyana alhininsu kan wannan rashi da kuma halin ƙuncin da ya fuskanta kafin rasuwarsa.

A cewar iyalan nasa, Farfesa El-Jummah ya rasu ne da misalin ƙarfe 2:45 na tsakar daren ranar Laraba, bayan wata gajeriyar rashin lafiya da ake zargin ta samo asali ne daga mawuyacin hali da wahalhalun da ya sha tsawon lokacin da yake tsare. Sun ƙara da cewa, an yi masa jana’iza bisa koyarwar addinin Musulunci.

Haka zalika, iyalan sun sanar da cewa za a gudanar da Sallar Gha’ib ga marigayin ranar Alhamis, 12 ga Fabrairu, 2026, da misalin ƙarfe 2:00 na rana a Masallacin Juma’a na Ngomari Old Airport da ke bayan gidansa a Maiduguri, inda suka buƙaci ‘yan uwa, abokai da sauran masu fatan alheri su halarta domin yi masa addu’a.

Tun daga shekarar 2009, Nijeriya ke fama da hare-haren Boko Haram da makamantansu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba wasu da muhallansu a sassan Arewa maso Gabas da ma ƙasashen makwabta irin su Kamaru, Chadi da Nijar.

Rasuwar Farfesa El-Jummah ta sake jaddada ƙalubalen tsaro da al’umma ke fuskanta a yankunan da hare-haren ‘yan tada ƙayar baya suka yi ƙamari, musamman kan manyan hanyoyi da ake yawan kai farmaki.

By ukarofi