Kungiyar RTEAN ta ci alwashin mara wa Tinubu baya a 2027

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ƙungiyar masu motocin sufuri da daukar ma’aikatan sufuri ta kasa, wato RTEAN ta ayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin babban zaɓen shekarar 2027, tare da buƙatar Gwamnatin Tarayya ta kafa wani Bankin Sufuri na musamman domin tallafa wa masu harkar sufuri a faɗin ƙasar nan.

An bayyana wannan matsaya ne a hedikwatar ƙasa ta ƙungiyar da ke Abuja ranar Alhamis, inda shugabannin ƙungiyar suka ce sun yanke shawarar ne bayan tuntuɓa mai zurfi da sassan ƙungiyar daga matakin rassa, jihohi, shiyyoyi har zuwa matakin ƙasa.

Shugaban RTEAN na ƙasa, Musa Maitakobi, a cikin sanarwar da aka fitar bayan taron, ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da na gine-gine da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa, musamman a ɓangaren sufuri, sun mayar da harkar sufuri ginshiƙi mai muhimmanci wajen bunƙasa ƙasa.

Ya ce, ɓangaren sufuri na buƙatar wani banki na musamman da zai fahimci yanayin harkar, domin bai wa masu zirga-zirga da dillalan sufuri damar samun rance cikin sauƙi don sabunta motoci, inganta kayayyakin more rayuwa, ƙarfafa tsaro da kuma faɗaɗa ayyukansu.

“Mun rubuta wa gwamnati domin ta yi la’akari da kafa Bankin Sufuri kamar yadda ake da Bankin Masana’antu da kuma Bankin Noma. Sufuri ya shafi ƙasa, teku da sama, don haka yana buƙatar tsari na musamman da zai tallafa masa yadda ya kamata,” inji Maitakobi.

ƙungiyar ta bayyana cewa manufofin gyaran da gwamnati mai ci ke aiwatarwa sun fi mayar da hankali kan tsari, daidaito, riƙon amana da kuma hangen nesa na dogon lokaci, wanda ya yi daidai da tsarin tafiyar da RTEAN a dukkan faɗin ƙasar nan.

A cewar ƙungiyar, a yau ba a kallon sufuri a matsayin wata hidima ta gefe ba, illa ana ganinta a matsayin ginshiƙin tsara tattalin arziki, wanda ke da tasiri kai tsaye kan kasuwanci, samar da ayyukan yi da jin daɗin al’umma.

“Idan sufuri ya tafi yadda ya kamata, tattalin arziki zai motsa, idan tattalin arziki ya motsa, al’umma za su ci gajiyar hakan. Wannan gwamnati ta fahimci muhimmancin sufuri wajen tabbatar da daidaito da ci gaban ƙasa,” inji sanarwar.

RTEAN ta jaddada cewa Nijeriya ba za ta iya ci gaba da siyasar gwaji ba, tana mai kira ga a tabbatar da ɗorewar shugabanci domin kammala ayyukan da aka fara da kuma kare jarin da masu ruwa da tsaki suka zuba a ɓangaren sufuri.

ƙungiyar ta kuma buƙaci mambobinta a faɗin ƙasar su fara shirin wayar da kan jama’a domin mara wa Tinubu baya a 2027, tana mai cewa daidaiton manufofi na da matuƙar muhimmanci wajen ɗorewar sauye-sauyen da ake yi.

Haka zalika, RTEAN ta yaba wa gwamnati kan ƙoƙarin bunƙasa amfani da iskar Gas ta CNG a matsayin madadin man fetur ga ababen hawa. 

Ta ce yawan motocin da ake gani a layukan cika gas a sassan ƙasar nan alama ce da ke nuna yadda masu sufuri ke karɓar wannan tsari.

ƙungiyar ta ce, shirin CNG ba wai na gwamnati kaɗai ba ne, illa shiri ne da ke amfanar masu sufuri kai tsaye ta hanyar rage kucin aiki da kuma inganta amfani da makamashi mai tsafta.

By ukarofi