El-Rufai ya ƙi yarda a kama shi

Spread the love

…Bayan isowarsa Nijeriya daga Masar

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ƙi yarda da yunƙurin jami’an tsaron Nijeriya na su kama shi a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da yake a Abuja a jiya Alhamis.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, a wani faifen bidiyo da aka wallafa a yanar gizo jiya, an ga El-Rufai yana magana da jami’an, waɗanda suka tunkare shi bayan ya sauka daga jirgi a yayin da ya ke dawowa daga Kairo, babban birni ƙasar Masar, amma sai tsohon gwamnan ya kafe kai da fata cewa, ba zai bi su ba har sai ya samu takardar gayyata a hukumance.

“Ku saurara, babu wanda, ko da shugaban ƙasa ne, da zai gaya min abin da zan yi. Idan ku na so ku gayyace ni, ku ba ni takardar gayyata a rubuce,” inji shi a cikin bidiyon.

Shi ma mai taimaka wa El-Rufai kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yanar gizo, ya tabbatar da yunƙurin da jami’an suka yi na kama El-Rufai, amma tsohon gwamnan ya ƙi yarda, yana mai neman a a gayyace shi a hukumance, amma bayan hakan sai suka karɓe fasfo ɗinsa daga hannun mai taimaka masa.

Sanarwar ta ce, “a yau jami’an tsaro sun yi yunƙurin kama Malam Nasir El-Rufai a yayin da ya ke dawowa daga birnin Kairo. Malam El-Rufai ya ƙi yarda ya bi su ba tare da izinin gayyata a hukumance ba. Don haka suka ƙwace fasfo ɗinsa daga wajen mai taimaka masa.”

Idan za a iya tunawa, a wata hira da El-Rufai ya yi da DCL Hausa, ya soki Mashawarcin Shugaban ƙasa kan Tsaron ƙasa, Malam Nuhu Ribaɗu, da bayar da umarnin a riƙa kama mutane ba tare da gudanar da bincike ba.

A ta bakinsa, “kawai sai Nuhu Ribaɗu ya riƙa ɗaukar waya yana kiran hukumomin tsaro don su kama kowa ba tare da gudanar da bincike ba.”

Ya jaddada cewa, “ba Ina cewa, Shugaban ƙasa ne yake yin kiran wayar ba,” yana mai ƙarin bayani da cewa, “ba aikin Mai Ba Wa Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro ba ne ya riƙa kiran EFCC, yana umartar su da suka riƙa kama mutum ko wani abu ba. Aikinsa shine, ya bai wa Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.

“Idan ya ga wani mutum wanda ya zama barazana ga tsaro, aikinsa shine, ya janyo hankalin Shugaban ƙasa kuma ya bayar da umarnin a yi bincike.”

Bugu da ƙari, El-Rufai ya zargi Ribaɗu da tsoma hannu kan harkokin shari’a ta hanyar yin tasiri a batun bayar da beli, yana mai cewa, yana neman alƙalai su bayar da beli ga waɗanda ake zargi ba tare da gudanar da cikakken bincike ba tun farko.

“Na kan ji kunya idan na tuna cewa, tsohon aboki ne shi,” inji El-Rufai, “babu wani maƙetaci a gwamnatin Tinubu kamar Nuhu Ribaɗu.”

Har kawo wallafa wannan rahoto hukumomin tsaro ko ofishin. Mashawarcin Shugaban ƙasa kan Tsaron ƙasa ba su mayar da martani ba.

By ukarofi