
Daga BELLO A. BABAJI
An samu tsaiko a yayin tantance maniyyatan Nijeriya a Madinah sakamakon haihuwa da wata maniyyaciya daga Jihar Zamfara ta yi a ranar Talata.
Hakan ya saɓa wa dokar ƙasar, wadda ta haramta wa mai juna biyu shiga sahun masu aikin hajji.
Hukumar ƙasar ta ‘Kingdom of Saudi Arabia’ da Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) sun sha yin gargaɗi musamman a ɓangaren lamuran da suka shafi lafiya waɗanda a ciki akwai hana mata masu juna biyu zuwa hajji.
Saidai, duk da haka akan samu ire-iren batun daga maniyyatan Nijeriya a lokuta da dama duk da gargaɗinda ake yi.
Daga cikin dokokin hajjin 2025 da Ma’aikatar Lafiya ta Saudiyya ta fitar akwai haramta wa mata masu juna biyu waɗanda watanni biyu ne tsakanin su da haihuwa da waɗanda ke fama da laulayi a yayin ɗaukar ciki zuwa aikin hajji.
Hukumar ƙasar ta ce, ta yi hakan ne da nufin tabbatar da bada kariya ga maniyyatan da rage adadin kiran agajin gaggawa a lokacin aikin hajji.
Haka ma masu cutuka da suka shafi na ƙoda, zuciya, huhu, hanta, daji, tarin fuka da dai sauran su.
A Nijeriya, NAHCON ta shar’anta yin gwajin juna biyu ga maniyyata mata da sauran ķa’idodin tantancewa, waɗanda sai an cika su, sannan za a bai wa maniyyaciya damar tafiya ƙasa mai tsarki.
Saidai duk da haka, jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, ba a samu cike sharuɗɗan ba daga hukumomin jigilar alhazai na jihohi yadda suka dace, wanda hakan saɓa wa dokar NAHCON ne da kuma na Saudiyya.
