Yadda rikicin Majalisar Dokokin Filato ya ƙazance

*Rigimar ta ci kujerar Kwamishinan ’Yan Sandan jihar
*Tsohon gwamna ya yi barazanar zanga-zanga

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Tun bayan da rikici tsakanin mambobin Majalisar Dokokin Jihar Filato ya tashi, inda ta kai da iƙirarin tsige Kakakin Majalisar, daga dukkan alamu rikicin ya na nema ya zama ba irin wanda aka saba gani ba, inda yanzu haka ya ci kujerar Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, wanda shi ba mamba ba ne a cikin majalisar.

Babban Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, IGP Usman Alkali Baba, ya bayar da umarnin cewa, a gaggauta kawo Bartholomew Nnamdi Onyeka ofishin rundunar ’yan sandan Jihar Filato a matsayin sabon kwamishinan ’yan sanda.

A cewar mai magana da yawun rundunar, kwamishina Frank Mba, ya fara aikinsa ne nan take bayan ayyana shi, sannan kuma aka tura kwamishina Edward Egbuka zuwa hedikwatar rundunar domin gudanar da wasu ayyuka na ƙasa.

Zai iya yiyuwa hakan ba zai rasa nasaba da rikicin shugabanci da ake fama da shi a Majalisar Dokokin Jihar ba.

A halin da ake ciki yanzu, rundunar ’yan sanda ta rufe harabar majalisar yayin da ɓangarorin biyu na ’yan majalisar ke ci gaba da yin ikirarin neman shugabancin majalisar.

Tun daga makon da ya gabata cece-ku-ce a tsakanin ɓangarorin biyu a zauren majalisar ke ƙara taɓarvarewa.

Kakakin majalisar, Abok Ayuba, wanda aka ce an tsige shi a ranar 27 ga watan Oktoba, 8 daga cikin 24 na majalisar, kuma ba tare da yin kaca-kaca da majalisar ba, ya jagoranci wani ɓangare na ’yan majalisar da ke goyon bayansa inda suka yi wani zama a wajen harabar majalisar da ƙananan kaya da silifas a ranar da aka tsige shi, ya kuma dakatar da ’yan majalisar da suka tsige shi, yana mai cewa shi ne sahihin shugaban majalisar.

A farkon makon ne Ayuba da ’yan majalisa masu biyayya, suka kutsa kai cikin harabar majalisar da ƙarfin tsiya, kuma suna gudanar da shirye-shiryen zama na zartaswa, inda aka girke jami’an tsaro masu yawa a harabar majalisar ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ’yan sandan Jihar, Edward Egbuka.

Jami’an tsaron sun yi awon gaba da Ayuba da magoya bayansa zuwa inda ba a san wajen da su ke ba.

Sai dai kwamishinan ya kwashe Ayuba tare da ’yan majalisar da ke mara masa baya daga harabar majalisar, inda ya bai wa Yakubu Sanda, sabon shugaban majalisar da masu biyayya gare shi.

Sanda ya yi wata ’yar gajeriyar zama tare da ɓangarensa sannan kuma ya ayyana kansa a matsayin sahihin Kakakin Majalisa.

Ya kuma bayyana cewa, zai ci gaba da jagorantar majalisar, amma hakan bai samu ba domin a yanzu ’yan sanda sun mamaye majalisar tare da hana wata ƙungiya zama.

Sai dai kuma tsohon gwamnan Jihar, Sanata Jonah Jang ya yi barazanar jagorantar zanga-zangar nuna adawa da haramtacciyar majalisar da al’ummar Filato za su yi.