Wata gimbiya ‘yar gidan sarauta ta yi watsi da dukan jin daɗin masarautar, inda kuma ta auri wani talaka gama-gari. Wannan na zuwa ne bayan haɗuwarsu a shekarar 2012 a makaranta, lamarin mai ban sha’awa, jama’a sun yi tsokaci sosai kan masoyan, inda aka tattaro maganar jama’a kan batun.
Tashar Aljazeera ta ruwaito cewa, za a ɗaura auren gimbiya Mako ta ƙasar Japan da wani talaka mai suna Kei Komuro a watan Oktoba na 2021.
A baya kaɗan, an lura cewa ma’auratan sun yi ta yawo a intanet kwanakin da suka gabata bayan dangantakarsu ta zama sananniya ga jama’a.
Ta bar sarautarta saboda talaka domin ta auri mutumin da kowa ya san gama-gari ne kuma talaka, gimbiyar za ta ba da matsayin sarauta da gadon ta da ya kai biliyoyin kuɗaɗe.
A wani faifan bidiyo da Aljazeera ta yaɗa, ma’auratan sun haɗu da juna ne a shekarar 2012. An ce Komuro wanda lauya ne da ake fafatawa da shi a ƙasar Amurka.
Yadda suka shirya aurensu, an soke shirin ma’auratan na yin aure a shekarar 2018, bayan rahotanni da aka samu sun ce dangin angon na fuskantar matsalar kuɗi.
Ko da yake a ƙasar Japan ana tuɓe mace daga sarautarta lokacin da ta buƙaci auren talaka, hakan bai shafi maza ba. Rashin samun isassun maza a cikin iyali yana haifar da rikicin maye gurbinsu.