Buhari ya gana da shugabannin tsaron Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

A ranar Alhamis da ta gabata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawa da shugabannin tsaro na Nijeriya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Duk da yake ba a bayar da cikakken bayani a hukumance ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, amma akwai yiwuwar tattauna batun ƙalubalen sakandar da ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga ke yi, wanda a yanzu haka ta zama wani alaƙaƙai a ƙasar, musamman a Jihohin Arewa maso yamma.

Daga cikin waɗanda ke wurin taron akwai mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo; Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami; Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (Mai ritaya); Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama; shugaban ma’aikatan shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari; da mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (Mai ritaya).

Sauran su ne Shugaban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor; Shugaban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya; Shugaban Hafsan Sojojin Ruwa, Mataimakin Admiral Awwal Zubairu Gambo; Shugaban Hafsan Sojojin Sama, Air Marshal Isiaka Oladayo Amao; Shugaban Hukumar DSS, Yusuf Bichi; da kuma Babban Darakta na Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA), Ahmed Rufai Abubakar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *