Yadda wata nakasasshiyar tsohuwa ta mutu ta bar miliyoyin kuɗi

Daga WAKILINMU

Kamar dai yadda aka sani ne cewa abin mamaki ba ya ƙarewa a duniya, domin za mu iya ganin misalin hakan inda wata tsohuwa mabaraciya ta rasu ta bar Miliyoyin kuɗi tare tare da ƙarin wasu a cikin asusun ajiya na banki. Har bayan rasuwarta hannunta shanyayyu ne ga shi kuma ba ta iya tafiya.

An gano hakan ne bayan rasuwarta inda ‘yan sanda suka gano gawarta a cikin wata tsohuwar mota a Beirut babban birnin ƙasar Lebanon, sanann suka gano cewa ashe tana da ruwan kuɗi masu yawa da kuma ƙarin wasu a cikin asusun banki kamar yadda wata takardar ajiyarta ta nuna.

Tsohuwar da aka bayyana sunanta da Fatima Othman, ta rasu ta bar kuɗi kimanin Dalar Amurka $3,300 a cikin lalitarta da kuma ƙarin wasu Miliyan $1.1.

Kakakin ‘yan sandan, Joseph Musallem, ya shaida cewa, marigayyar ta rasu ne sakamakon bugun zuciya kuma ba a zargin ko farmaki aka kai mata. Amma sai dai sun yi mutuƙar mamakin ganin cewa ta mallaki irin waɗannan maƙudan kuɗaɗe.

Labarin tsohuwar ya watsu ne tun bayan da wani hoton Soja yana bata ruwa tana sha ya ɓulla a yanar giza. A sakamakon hakan ne shi ma Sojan kwamandansa ya yaba masa a dalilin halin jinƙai da taimakon ɗan Adam da ya yi.

Yanzu haka dai jami’an ‘yan sandan sun miƙa gawarta bayan sun lalubo dangin Marigayyar a wani gari mai suna Ain Al-Zahab da ke Akkar a Arewacin ƙasar ta Lebanon, kuma har an binne ta.